Jam'iyyar PDP ta shirya kwace Jihar Edo

Jam'iyyar PDP ta shirya kwace Jihar Edo

-Jam'iyyar APC tayi zaben firamare dinta a ranar asabar 18 ga watan yuni a filin kwallon kafan Samuel ogbemudia dake benin city, babbar birnin jihar edo.

-A bangare daya, jam'yyar adawa PDP tana gudanar da zabenta na firamare na takarar zaben gwamnan jihar da za'ayi a watan satumba 2016.

-Sama da wakilai 740 za suyi zaben a yau litinin 20 ga watan yuni.

Jam'iyyar PDP ta shirya kwace Jihar Edo

Kimanin daliget 740 ne aka tantance domin kada kuri'arsu a karkashin leman PDP a yau litinin 20 ga watan yuni domin zaben firamare na fidda gwanin da zai yi takaran a zaben gwamnan Jihar Edo da za'ayi a watan Satumba.

An fara ne da tantance masu kada kuri'a da misalin karfe 9:30 na safe a wurare daban daban guda 3, yayinda wakilan Mazabar Edo ta kudu na gudanar da na ta a Okada House, wakilan mazabar Edo Ta Arewa na yin nasu  a JBS Estate, wakilan mazabar Edo ta tsakiya kuma na yin na su a Sakatariyan Jam'iyyar. Masu takaran kujeran Gwamnan karkashin leman Jam'iyyar PDP da suka saya fom a Hedkwatan jam'iyyar akan naira 16 miliyan su ne, Chif Solomon Edebiri , Mr Osagie Ize-Iyamu da Mr Mathew uduoeyekemwen  dukansu daga mazabar Edo ta kudu.

Shugaban zaben gwamnan jihar ebonyi Umahi ya sanar cewa idan aka gama tantance wakilai a wurare 3, to duk za'a hadu a filin kwallon kafar Samuel Ogbemudia inda jam'iyyar APC tayi nata, akwai kwamiti ba muam da aka ranstar domin shirya su .Gwamna umahi ya baiwa masu takara, da wakilai da sauran yan jam'iyyar tabbacin cewaza'a gudanar da zaben cikin kwanciyan hankali da lumana.

KU KARANTA: EFCC ta kama tsohon shugaban NNPC, Jide omokore

Daya daga cikin masu takaran Ize -Iyamu ya taba sakataren gwamnan jihar karkashin Gwamna Lucky Igbinedion . Shi kuma uduoeywmekemwen shine tsohon shugaban masu rinjaye ne a majalisar jihar. Kakakin jam’iyyar PDP ta jihar , Mr Chris Enehikhare, ya bayyana cewa an gudanar da zaben ne a bisa umurnin shugabancin Jam’iyyar ta kasa karkashin Senata Ahmad Muhammad MAKARFI.

A ranar lahadi kuwa ,19 ga watan yuni Godwin Obaseki wanda ma’akataci ne karkashin shugabancin gwamna Adams oshiomole ne ya lashe zaben firamaren Jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel