Arsene Wenger ya bayyanar da muradun sa

Arsene Wenger ya bayyanar da muradun sa

Koci Arsene Wenger ya bayyanar da muradun sa na sayayyen ‘yan wasa.

 – Kulob din na Arsenal sun saye dan wasa daya ne rak, cikin kakar sayyayen ‘yan wasan na bana.

 – Wenger ya bayyana Shirye-shiryen da yake yi.

 – Tauraron dan wasan Leicester ya ce ‘Ba shi ba zuwa Arsenal’

Arsene Wenger ya bayyanar da muradun sa
Wenger

Mai kula da kuma horas da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafar Arsenal ta Ingila yace bai so ya yamutsa fasalin kungiyar da sayen ‘yan wasa ratata. Arsenal din dai tuni ta saye dan wasan nan na Kasar Switzerland mai buga ma kulob din Borussia Mochenglabach da ke Kasar Jamus, Granit Xhaka. Xhaka din dan wasan tsakiya ne. Ba shakka ‘Yan Arsenal din za su ji dadin sayen Xhakan don kuwa rikakken dan wasan tsakiya ne; mai tare da duka, ga shi da wata bahaguwa mai karfin jaraba.

Lokacin da aka tambayi Wenger game da sayen wasu ‘yan wasan, sai yake cewa: “Ba za mu yi sayayya barkatai ba, mun sayi dan wasa guda-Granit Xhaka daga Borussia Mochenglabach. Haka kuma mun rasa guda 3; Mikel Arteta, Tomas Rosicky, da kuma Mathieu Flamini”

Toh kun ga mun saye daya, kuma muna cikin kasuwar, mu samu mu kara sayen daya ko biyu. Ba abu ne mai sauki ba hakan, amma kuma dole muyi la’akari da ‘yan wasan mu. Idan aka saye ‘yan wasa rututu sai ya rikita kan gadon kungiya. Dalili ba za mu saye ‘yan wasa sama da 3 ba.

 

Arsene Wenger mai horar da kungiyar Arsenal da ke Landan a wani wasan sa da kungiyar Chlesea.

Hakanan kuma Jamie Vardy ya yanke shawarar zama a kulob din sa Leicester duk da Arsenal din sun neme sa. Wenger yake cewa “Vardy dai a yanzu haka yana Leicester, kuma iya sani na zai yi zaman sa a can.”

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel