Mutane 15 sun rasa ran su a kan titin Legas zuwa Ibadan

Mutane 15 sun rasa ran su a kan titin Legas zuwa Ibadan

- Mutane 15 sun rasa ran su a kan titin Legas zuwa Ibadan.

 – A yayin da mutanen duniya ke biki murnar mahaifan su ranar 19 ga watan Yuni.

 – Wasu kuma zaman makoki suke yi.

 – Wani hadari a kan babban titin Legas zuwa Ibadan yayi sanadiyar rayuwaka da dama.

Mutane 15 sun rasa ran su a kan titin Legas zuwa Ibadan

Wani hadari da ya auku a ranar 19 ga wannan watan na Yuni kan babban titin nan na Legas zuwa Ibadan yayi sanadiyar ajalin mutane 15. Jaridar ‘The Nation’ ta rahoto wannan labari. Sai dai jaridar Punch ita kuma a nata, tace mutane 19 suka mutu, New Telegraph kuma ta rahoto cewa mutane 14 ne suka riga mu gidan gaskiya. Hadarin ya auku ne tsakanin wata babbar motar-mai da kuma wata mota kirar bas a daidai ‘Fidiwo-Ajebo’, cikin Jihar Ogun kan hanyar Legas zuwa Ibadan.

 

Ga mummunan hoton abin da ya auku. Daukar Hoto: Jaridar The Punch

Wata gingimari mai lambar AJG 40 XA, da kuma motar-mai mai lamba RAN 571 XA da kuma wata karamar motar bas ta haya mai lamba AGL 373 XR suka yi hadarin. Abin dai ya faru ne lokacin da direban motar-man wanda ke nufin zuwa garin Ibadan yayi yunkurin wuce wata gingimari kusa da inda ake kan aikin gyaran hanyar. Babbar motar ta afka ma motar hayar inda mutum daya kacal ya tsira.

Jami’in hukumar kula da dokokin titi na Jihar Ogun watau TRACE mai suna Babatunde Akinbiyi ya tabbatar da wannan mummunan abu.

Yake bayani cewa ana gyaran ne kan hanyar, shi ya sa aka raba hanyar. Yace jami’an TRACE da ta hukumar kasa ta FRSC da kuma ‘yan Sanda suka tsamo wadanda abin ya fada ma wa. Cikin mutane 15 din da suka mutu; akwai mata 6 da maza 9, yayin da mutum daya ya samu raunuka. Kokarin kutse ne inda bai dace ba ya jawo wannan hatsari Inji Babtunde. Tuni shi kuma wanda ya samu raunin aka garzaya da shi asibitin Koyar da ma’aikata na Jami’ar Olabisi Onabanjo da ke garin Sagamu. An kuma ajiye gawan sauran a gidan ajiye gawawwaki da ke Ipara, kusa da garin Sagamu.

Haka wancan makon da ya gabata mutane 10 suka mutu, inda 23 kuma suka raunata a wasu hadaurran motan da suka auku a ranar Laraba da Alhamis.

 

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel