Ana fada tsakanin Ijaw da kungiyar yan'bindiga

Ana fada tsakanin Ijaw da kungiyar yan'bindiga

Legit.ng ta rahoto cewa, Rikici ya kaure a tsakanin al'umman Ijaw mazauna yankin, da kuma yan'bindiga a Agbeded, karamar hukumar Ikorodu na jihar Legas.

Ana fada tsakanin Ijaw da kungiyar yan'bindiga
Yan bindiga dadi

A halin yanzu da rahoto ke zuwa, babu wanda ya san abunda ya haddasa wannan rikici, Legit.ng ta tabbatar da cewa, kwamishinan yan'sanda na jihar Legas ya aika da rundunan jami'an yan'sanda zuwa yankin.

An yi kokarin sanar da Lagos state police Public relations officer, amma hakan bai samu ba saboda nambar wayar salula dinta da ya ki shiga.

KU KARANTA KUMA: An kama masu neman aikin yan’sanda biyar

ku tuna cewa, yan'bindiga sun kai hari ga al'umman jihar Ogun kwanan nan, inda suka kashe mutane 15. Yan'sanda sun bayyana cewa, yan'bindigan sun zo ne daga yankin Niger Delta. Kasar na fuskantar hare-hare da dama daga yan bindiga a kwanakin nan.

Har ila yau, kwamishinan yan'sanda na jihar Ogun, ya ce, yan'bindiga sun tsare hanyar Lagos-Ibadan expressway.

A makon da ta shige kuma, An rahoto cewa, wasu yan’bindiga sun kai hari, gidan dalibai mai suna ‘Gidan Grace and Mercy’, wanda ke hanyar Health Centre, Omuokiri, a karamar hukumar Ikwerre na jihar. An kuma ce sun kai hari a dakuna 8, daga cikin dakuna 9 da ke gidan, kuma sun tafi da abubuwa kamar: Na’ura mai kwakwalwa, wayoyin salula, ATM carda, kayayyakin sa wa, kudadem da sauran abubuwan amfani.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel