Sojojin Najeriya da 'yan sa-kai sun kashe yan Boko Haram a Borno

Sojojin Najeriya da 'yan sa-kai sun kashe yan Boko Haram a Borno

Sakamakon wani hadin gwiwar da akayi tsakanin sojin Najeriya dake bataliya ta 114 da kuma sojojin sakai da kuma yan kato-da-gora a ranar lahadi 19 ga wata sun kai samame a garin Bitta-Damboa.

Wata sanarwar da rundunar sojojin ta fitar ta ce sojojin sun kaddamar da wani hari daga garin Bitta har Gambori dake jihar Borno.

Sanarwar ta cigaba da cewa yayin samamen da aka kai anyi arangama da yan ta'addan Boko Haram din a kauyen Bulajani inda kuma aka samu nasarar kora tare da kashi su baki daya.

Sojoji da 'yan sa-kai sun kashe yan Boko Haram a Bitta 

dan boko haram

KU KARANTA: Mumbarin yan PDP ya rufta da dan takarar gwamna a Kebbi

Abun takaici kuma shine kamar yadda sanarwar tace shine sojoji 5 sun samu raunuka sannan kuma motar su ta lalace sosai. Sojojin kuma sun ce sun kashe yan ta'addan guda hudu sannan kuma wasu da yawa sun gudu da ciwuka da dama.

Sanarwar ta ciga ba da cewa: "Lokacin samamen an samu nasarar kwato babura 6 da kuma abinci mai yawa. Sannan kuma an kwato bamabamai da yawa a kauyen Madube".

"Sojojin da suka samu raunuka kuma tuni an kaisu asibiti ta 23 dake garin Yola."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel