Sakamako da rahotannin wasannin NPFL: Sati na 23

Sakamako da rahotannin wasannin NPFL: Sati na 23

Sakamako da rahotannin wasannin NPFL: Sati na 23

MFM FC 0-1 3SC

Kulob di shooting stars dake garin Ibadan a ranar Lahadi sun samu nasarar su ta farko wajen gida a kan kungiyar MFM FC da ci daya mai ban haushi a garin Agege dake Lagos.

Dan wasa Ebitimi Agogu's ne dai ya jefa kwallon a minti na 83.

 

Niger Tornadoes 1-1 Enugu Rangers

Kulob din Niger Tornadoes suna cizon yatsa sakamakon kunnen doki da sukayi da kulob din Enugu Rangers a garin Minna sakamakon rashin katabus din da sukayi.

Mustapha Musa ne dai ya fara jefa musu kwallo kafin daga bisani Osas Okoro ya rama a minti na 90.

 

Abia Warriors 1-0 Heartland

Bayan rashin nasarar da sukayi a wasannain su biyu da suka gabata, Uche Ihurulam ne ya jefa ma kulob din na garin Abia kwallo a minti na 28 a garin Umuahia wanda shine ya basu maki 3.

 

Ifeanyi Ubah FC 2-0 Rivers United

Tsohon dan wasan gaban 3SC Wasiu Jimoh shine ya ji kwallon shi ta farko a kuma wasan shi na farko da kulob din Ifeanyi Uba din a minti na 23 kafin daga bisani Ismaila Gata ya kara jefa wata kwallon

 

Akwa United 2-0 El-kanemi Warriors

Kungiyar Akwa United dai tana ci gaba da buga kakar wasannin ta da kyau a inda ta lallasa El-kanemi Warriors da ci 2. Micheal Ikpe ne yaci kwallon.             Ku Karanta: Labari da dumi dumi

 

Wikki Tourist -3-1 Kano Pillars

Kungiyar Wikki ta garin Bauchi ta cigaba da kare gidan ta inda ta lallasa Kano Pillars da ci 3 da 1. Kungiyar ta Kano ita ce dai ta fara jefa kwallo kafin Wikki Tourist din ta zo ta rama sannan kuma ta kara har biyu.

Emmanuel Edmund ne ya fara jefa ma Kano Pillars din a minti na 35 kafin Ibrahim Alhassan ya rama, Abubakar ya kara sannan kuma Alhassan din ya kara.

 

Wani labarin kuma na nuna cewa wasa tsakanin Warri Wolves da Plateau united an daga shi sai yau litinin 20 ga wata saboda mamakon ruwan sama da akayi a garin Warri.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel