Babu kariya,babu fensho ga ‘yan Majalisa – SERAP,Falana

Babu kariya,babu fensho ga ‘yan Majalisa – SERAP,Falana

- Kungiyar yaki da rashawa SERAP ta yi turr da yunkurin bai wa yan majalisa kariya da fensho ta din din din

- Femi falana yace yunkurin samun kariya da fensho ta din din din wa yan majalisan tarayya, kololuwan rashin hankali, rashin kunya da rashin basira ne.

- Debo adeniran ya ce yan majalisan da je neman kariyan su ne wadanda suka aikata mafi mumunan laifin rashawa kuma suna kokarin guje wa.

- Majalisa tarayya na yunkurin bada kariya da fensho ta kare rayuwa wa shuwagabannin ta.

Babu kariya,babu fensho ga ‘yan Majalisa – SERAP,Falana
Femi Falana (SAN),

Kungiyar SERAP, da lauyan kare hakkin bil adama , Mr Femi Falana sunyi turr da yunkurin samarwa shuwagabannin majalisa tarayya kariya da fensho ta kare rayuwa. A yayinda Kungiyar SERAP ta siffanta wannan yunkuri a matsayin rashin adalci da kuma shirin sake kuntata wa masu dogaro da fensho wadanda an hana su hakkin su bayan sun manyanta, shi Femi Falana yace wannan kololuwan rashin hankali da rashin kunya ne.

Wannan samarwa shuwagabannin yan Majalisan kariya da fensho ta kare rayuwa ya faru ne a yayinda kwamitin majalisan dattawa akan gyare gyaren kundin tsarin mulki ta gana a legas a ranan asabar. SERAP, a wani jawabin da direktan Kungiyar,Adetokunbo Mumini ,

“ Wannan samarwan  kokarin yin amfani da karfin majalisa domin chanja kundin tsarin mulki na 1999  domin ci ma burin kan su  da kuma cin karansu ba babbaka.  Baiwa senatoci da yan majalisan wakilai kariya da fensho ta kare rayuwa ba ta da alaka da cigaban kasa ko al'ummata.

KU KARANTA: Ofishin ‘yan sanda ta gayyaci David Mark da Ekweremadu

Femi Falana, yayinda ya ke hira da Jaridar Punch, ya ce:

“Wannan samarwan a lokacin da kudin albashi ma ya gagara biya, wannan samarwan kololuwan rashin hankali, rashin kunya da batan basira ne. Lallai fa batan basira ne, a lokacin jihohin da yawa sun gaza biyan biyan ma'akata albashi, shine ake kawo maganar ba su fensho ta kare rayuwa. Wannan samarwan kariyan kuma abin ban haushi ne da takaici. Ba kasa mai hankali da zata baiwa yan Majalisan da ke tuhumar cin hanci , rashawa, aikin yan jabu, da fyade  kariya. Muna tabbatar wa yan najeriya cewa wannan shedaniyar yunkurin ba zata yiwu ba. Kuma yana da muhimmanci a sanar ma yan majalisan cewan , yan yakin kare hakkin bil adama na shirin hada zanga zanga domin watsi da wannan mugunyar samarwa.

Bugu da kari, direktan Kungiyar CACOL, debo adeniran yace, “Masu neman ma shuwagabannin majalisa kariya sune dai wadanda ke san ganin karshen hukumomin yaki da rashawa. Wannan na zuwa ne a lokacin da  yan najeriya na neman a cire maganan bada kariya daga kundin tsarin mulki domin shawo kan rashawa da al mundahana. Debo adeniran ya ce yan majalisan da ke neman kariyan su ne wadanda suka aikata mafi mumunan laifin rashawa kuma suna kokarin guje wa, kuma masu neman fensho ne barayin gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel