Deeper Life sun bukaci yan'Najeriya da su yi hakuri

Deeper Life sun bukaci yan'Najeriya da su yi hakuri

- Cocin Deeper Life sun nemi yan'Najeriya da su ba gwamnatin Buhari goyon baya

- Cocin sun bayyana gamsuwarsu na cewa shugaban kasa zai iya tafiyar da al'amuran kasar

- Cocin sun kuma karfafa wa shugaban kasa Buhari gwiwa kan ya sadar da rara na mulkin demokradiyya

Deeper Life sun bukaci yan'Najeriya da su yi hakuri

Kungiyar Deeper Life Bible Church, sun aika sako zuwa ga yan'Najeriya na bukatan su kara hakuri da Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Gwamnatin Buhari na fuskantar kalubale da dama tare da matsalar tattalin arziki, wanda ya janyo faduwar naira da ci gaban fashe fashen bututun man petir a yankin Niger Delta.

KU KARANTA KUMA: Cardinal Okojie ya gargadi Buhari

Jaridar Leadership ta rahoto cewa, babban malamin kirista Pasto Joshua O. Esho, wadda shine mai fada a ji a cocin na tarayya, ya roki yan'Najeriya da su yi hakuri da Buhari, kamar yadda yake kokarin kawo canji a kasar, da son dawo da kasar kamar yanda take a da.

Pasto din ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni, a wata jawabi da cocin ta shirya, na addu'an dare, mai lakanin "Night of Extraordinary Wonders", wanda akayi a birnintarayya Abuja daga masu fada a ji a cocin, Pasto W.F. Kumuyi.

Duk da haka, Esho y bukaci gwamnatin da ta zama mai sauraron mutane, kuma suyi aikata duk abunda zai yiwu a gajeren lokaci, don rage wahalhalun da talakawa ke ciki, daidai da alkawuran da ya dauka lokacin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel