Yan Super Eagles 3 za su ci gaba da taka leda a Chelsea

Yan Super Eagles 3 za su ci gaba da taka leda a Chelsea

- Yan Super Eagles 3 za su ci gaba da taka leda a Chelsea badi.

 – ‘Yan wasan Najeriya: Victor Moses, Omeruo da kuma Mikel Obi za su cigaba da taka leda a Kulob din Chelsea din badi.

 – ‘Yan wasan su uku za su samu lokacin buga wasa karkashin sabon mai horaswa, Antonio Conte.

 – Yara masu tasowa irin su Dominic Solanke, Ugbo Ike da Tomori Fikayo za su cigaba da buga ma Kulob din Chelsea din.

Yan Super Eagles 3 za su ci gaba da taka leda a Chelsea
John Obi Mikel

Kungiyar Ingilar ta Chelsea ta fitar da sunayen ‘yan wasan da ta saki na shekarar wasa mai gabata, inda ya nuna cewa Victor Moses, Omeruo da kuma Mikel Obi za su cigaba da zama a Chelsea din zuwa badi.

Dan wasan Kungiyar Chelsea ke nan yayin da yake taka ledar a wani wasa. Shi dai John Mikel Obi din ya dade a kungiyar Chelsea, tun shekarar 2006 ake bugawa da shi, su kuma Victor Moses da Omeruo an sha bada aron su zuwa wata kungiya.

Kungiyar Kasimpasa ta karbi aron Omeruo wancan shekarar, shi kuma Moses kungiyar ingilar West Ham ce ta karbi aron sa. Ana ganin cewa sabon kocin kulob din Antonio Conte na da shirin yin amfani da ‘yan wasan 3, za ya basu dama su zuba tasu rawar ya gani.

Mai horar da ‘yan wasa, Antonio Conte

Kulobs daga kasashen Sin da ma Turkiyya suna ta neman a saida masu mai rike da kambun kungiyar kwallon kafar Najeriya, Kyaftin Mikel. Amma har way au ba a sani ba ko zai bar kulob din Chelsea da ya shafe shekaru 10 da su ko zai motsa daga birnin na Landan.

Wasu ‘yan wasan masu jinin Najeriya da za su cigaba da wasa a Chelsea din sun hada da Dominic Ayodele Solanke, wanda ya buga wasa a kulob din Vitesse Arnhem da ke kasar Holan. Da kuma Ugbo Ike da Tomori Fikayo. Har way au ana faman tattaunawa da Olu Aina kan sabon kwantiragi.

Kulob din Chelsea din dai ta kare wasan kakar banan nan ne da maki 50 cikin wasanni 38 da ta doka.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel