Tsohon ministan Obanikoro yayi tsokaci daga mabuyarsa

Tsohon ministan Obanikoro yayi tsokaci daga mabuyarsa

- Tsohon karamin ministan tsaron tarayyan Najeriya karkashin mulkin PDP Musiliu Obanikoro yayi korafi daga mabuyarsa America yana sukan gwamnatin APC karkashin shugaba Buhari akan sumamen da jami'an hukumar EFCC suka kai gidajensa da na yayansa dake Lagos.

Tsohon ministan Obanikoro yayi tsokaci daga mabuyarsa
Tsohon ministan tsaro obanikoro

Obanikoro yayi amfani da shafin muhawara ta gaban gizo wadda ake kira twitter son suka da mayar da martani akan yunkurin hukumar EFCC yana kazafi akan tsarin mulkin shugaba Buhari inda ya danganta shi da mulkin danniya da tauye hakkokin al'umma da kama karya Wanda ba zai haifar da da mai ido ba zai zai jefa talakawar cikin mawuyacin bakin kunci da talauci kamar yadda shugaba Buhari aka sanshi dashi bayan ya mulkin kasan a tsaron mulkin Soja. Hukumar EFCC tana tuhumar tsohon ministan akan almundahana da kudaden kasa da kuma murdiyan kwandiloli ayanzu ana radi radin fito da sammacin dawo dashi daga mabuyarsa.

Hukumar EFCC tana binciken manyan jami'an gwamnatin data shuda karkashin Goodluck Jonathan ayunkurinta na kawar da rashawa a Najeriya don tafiyar da ingantancen mu'amala tsakanin gwamnatin da al'ummar kasa. Almiblan jam'iyyar APC mai ci yanzu dai bisa dukkan alamu ya sha banban da ta jam'iyyar hamayya PDP Wanda suke rike da madafun iko tun 1999.

Asali: Legit.ng

Online view pixel