Wenger ne yasa na zo Arsenal inji Ozil

Wenger ne yasa na zo Arsenal inji Ozil

Dan wasan tsakiya na kulob din Arsenal Mesut Ozil ya nuna girmamawar sa ga kocin sa Arsene Wenger yayin da ya bayyana cewar kocin dan kasar Faransa ne ya sanya shi zuwa kulob din.

Wenger ne yasa na zo Arsenal inji Ozil
Mesut Ozil

Ozil din ya bayyana wa kafar yada labarai ta yanar gizon Joe.co.uk cewar Wenger ne musabbabin dawowar tasa. Ozil yace: "shi Wenger yana da kwarjini. Kuma irin mutanen nan ne da zasu fada maka hakikanin abun da suke so kayi da kuma bari a cikin fili."

KU KARANTA: Boko haram ta bude gidan Rediyo - VOA Hausa

"Daga karshe da sai na yanke shawarar kawai in taho Arsenal din saboda in samu kasancewa da shi don nasan zai taimaka mun a ko yaushe.

Dan kwallon tsakiyar kuma ya fada ma kafar labaran cewar farkon zuwan shi ya dan samu tsaiko wajen koyon harshen turanci amma daga baya ya samu ya iya ta hanyar malanin da ya dauka. Shidai Ozil din ya dawo kulob din Arsenal ne cikin watan satumbar 2013 daga kulob din RealMadrid akan kudi £42.5m. Shi din kuma ya ci kofin FA har sau biyu a tsawon lokacin da ya dauka a kulob din.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel