PDP, APC, APGA duk ba sune mafitar Najeriya ba - SPN

PDP, APC, APGA duk ba sune mafitar Najeriya ba - SPN

Jam'iyyar yan gurguzu ta SPN watau Socialist Party of Nigeria tace gwamnatin shugaba Buhari bata da hanyoyin da zata gyara kasar nan.

PDP, APC, APGA duk ba sune mafitar Najeriya ba - SPN

Jaridar Punch ta ruwaito cewa jam'iyyar ta SPN ta kuma ce itama PDP da APGA duk basu da hanyoyin gyara kasar. Jam'iyyar ta kara da cewa mutane sun zabi Buhari ne nisa tunanin zai magance musu matsalolin kasar tun daga rashin aiki zuwa tabarbarewar tattalin arzikin kasa amma har yanzu akasain hakan kawai suka gani.

Shugaban jam'iyyar ta SPN Segun Sango ya zargi shugaba Buhari da jayo ma mutane tsadar rayuwa da talauci. Shugaban jam'iyyar ya kara da cewa kudurorin gwamnatin Buhari duk na jari hujja ne kuma ba sune zasu gyara kasa ba.

Segun ya kara da cewa matsalolin Najeriya sun samo asaline tun daga yadda aka bi wajen hada arewaci da kudancin kasar. Shugaban SPN din ya kuma yi kira ga kungiyar 'yan kwadago NLC da ta tursasa ma gwamnati mallakar masana'antun da suke da alaka da talaka kai tsaye kamar bankuna, wutar lantarki da gidajen mai.

Ya kuma kara da cewa NLC din yakamata  tafara yajin aiki kan yadda ake kin biyan ma'aikata albashi tare kuma da neman karin albashin duk fadin kasar nan. A wani labarin mai kama da wannan, sakataren jam'iyyar APC Alhaji Mai Mala Buni ya ce  ba ruwan jam'iyyar da rikicin da PDP take ciki.

Source: Legit.ng

Online view pixel