Hukumar EFCC ta bakonci Modu sherrif don amsa tambayoyi

Hukumar EFCC ta bakonci Modu sherrif don amsa tambayoyi

-Hukumar EFCC ta gayyaci tsohon Gwamnan jihar Borno kuma shugaban bangaren hamayya a jam'iyyar PDP Senator Ali Modu Sherrif don masa tambayoyi akan kudaden makamai Wanda hukumar take zargin jam'iyyar PDP ta yi amfani dasu wajen yakin neman zaben shekaran 2015.

Hukumar EFCC ta bakonci Modu sherrif don amsa tambayoyi

Tsohon gwamnan jihar Borno Sanata Ali Modu Sherrif.

Hukumar tana zargin cewa tsohon gwamna Ali Modu Sherrif ya karba kudade daga ofishin tsohuwar ministan albarkatun mai Deizani Alison Maduekwe tsaban kudi million 450 a matsayin kason jihar Borneo wurin yakin neman zaben 2015. Hukumar kuma tana tuhumar tsohon gwamna Sherrif da karba tsaban zunzurutun kudade tsaban dallan America million 115 daga hannun Deizani Alison Maduekwe Wanda itama tana cikin jerin wa'inda hukumar take bincike akai.

"Wani jami'in hukumar Wanda ya sakaye sunansa yayi bayanin cewa tsohon Gwamnan ya kawo kansa ofishin hukumar EFCC dake Maiduguri da safiyan jiya laraba misalin karfe 10 kuma aka bada bailinsa tsakanin karfe 5:30 da yammacin amma da sharadin gayyato shi idan bukatan hakan ta taso. Jam'in ya kuma nuna cewa hukumar tana kuma binciken tsohon Gwamnan yayi bayanin yadda ya tafiyar da kusan billion 300 kudaden jihar Borno

Daga asusun tarayyan a lokacin wa'adin shekaru 8 da yake Gwamnan jihar.

Bisa dukkan alamu dai ruwa yayi tsami ga tsohon Gwamnan Borneo sanata Ali Modu Sherrif tunda uwar jam'iyyar sa ta PDP sashi suna adawa dashi kuma ga yunkurin da sukeyi na tunkude shi daga shugabancin jam'iyyar. Ita jam'iyyar PDP a yanzu ana iya cewa tana cikin tsaka mai wuya inda bagarori biyu suke ikrarin shugancin jam'iyyar. Wannan yanayi yana matukan kawo tsiko ga Ita jam'iyyar hamayya ta PDP ganin cewa zabbukan gwamnoni a jihohin Edo da Ondo suna karatowa.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel