Dole ayi ma Najeriya garambawul – Cewar Gani Adams

Dole ayi ma Najeriya garambawul – Cewar Gani Adams

–Shugaban Kungiyar OPC Gani Adams ya ba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari shawarar da ayi ma tsarin Kasar garambawul

–Adams yace dole yankuna su cigaba a nasu matakin ba tare da jiran gwamnatin tarayyar Kasar ba

–Gani Adams ya bayyana cewa wannan kuwa shine ra’ayoyin fiye da mutane miliyan biyar na ‘Ya ‘Yan kungiyar ta OPC

Dole ayi ma Najeriya garambawul – Cewar Gani Adams
Gwamna Adams Oshiomole

Gani Adams na so ayi canza tsarin Najeriyar. Shugaban Kungiyar Mutanen Odua watau OPC ya shiga cikin sahun masu bada shawarar a canza tsarin Kasar Najeriyar.

Gani Adams din ya yi wannan kiran ne karshen makon nan da ya gabata, a ranar bikin 12 na watan Yunin na. Ya ke cewa babu bukatar a kara tunawa Shugabannin Najeriya cewa lokacin da za duba shirin tsarin kasar nan yayi.

Yace: “Masu so a cigaba da tafiya a wannan turba sune kawai wadanda ke karuwa da gurbataccen tsarin. Sun fi son tsarin da sam babu gaskiya a cikin sa” Ya ke cewa, Babu yadda za a samu mutane na kwarai ba tare da an yi gini na kwarai din ba.

“Akwai bukatar a sani cewa dole fa a sake duba tsarin Najeriya, wannan shine matsaya ta da sauran miliyoyin ‘yan kungiyar OPC. Dole a gaggauta duba wannan.”

Adams yayi Tir da irin wannan tsarin gwamnati da ake yi a Najeriya, cewar an gama Najeriyar ne da karfi da yaji.

Tun kafin a kirkiri wannan kasa ta Najeriya, akwai kasar yarbawa tun karni na 11, Ile Ife kadai na da jama’a kusan mutum 70,000. Akwai sarakunan Habe na Hausa tun kafin jihadin Danfodiyo. Inji Gani Adams.

Akwai kuma masarautar Borno ta bare-bari. Ga kuma masarautar Benin wacce ta samo asali tun kafin a hada kasar a shekarar 1914. Haka suma Inyamurai suna da yankin su da masarautun Kasar su. Hadin gambizar game Kasar da aka yi a 1914 da karfi da yaji kawai don son ran turawan mulkin mallaka ne. Duk Inji Adams.

Gani Adams yace sam bai dace a ce tubalin mulkin duk Kasa a ce yana wajen wani mutum daya ba.

“’Yan Sanda, Soji, Kwastan da sauran su, hatta rajistan kamfanoni da lambar mota ace yana hannun gwamnatin Tarayya”

“Tattalin arzikin Kasa, tsarin ilmi da Jami’o’in Kasa duk suna karkashin gwamnatin tarayya.”

Abin kunya ne a ce Gwamnatin tarayya da ke sama ke kokarin rike da makaruntun firamare ta wata hukumar SUBEB, yake kuka da cewa wai sai an turo kudi daga Abuja zuwa makarantun kauyukan Ondo, Borno da jihohin Sakkwato.

Asali: Legit.ng

Online view pixel