Rikicin sa Hijab: An kwashi 'yan kallo a jihar Osun

Rikicin sa Hijab: An kwashi 'yan kallo a jihar Osun

An kwashi yan kallo a wasu makarantu biyu dake jihar Osun sakamakon wasu dalibai da suka je makarantun su da kayan coci.

Rikicin sa Hijab: An kwashi 'yan kallo a jihar Osun
Gwamna Rauf Aregbesola

Shi kuwa gwamnan jihar ta Osun Rauf aregbesola ya gargadi duk wani dalibin da karya dokar makaranta da kora. Kamfanin labarai na Premium Times ya ruwaito gwamnan yana bada kashedin jiya talata 14 da watan Yuni a wajen kaddamar da makarantar St. Micheal's RCM a garin Ibokun.

Tun farko dai kungiyar kiristicin kasar nan ta CAN ta umurci wasu kiristocin kasar da su sanya kayan su na coci in zasu makaranta indai har gwamnatin ta dage cewar mata musulmai ma su rika sa hijab idan zasu makaranta.

Ranar talata ne dai 14 ga watan June daliban kiristoci suka bayyana a makarantun nasu da kayan coci kafin daga bisani a kore su. Jami'an kungiyar CAN din kuma har zuwa sukayi makarantun domin tabbatar da cewa an bar daliban sun halarci azuzuwan su.

Da yake magantawa akan lamarin, gwamnan jihar ta Osun Aregbesola ya karyata zargin cewa yana katsalandan ne da hukuncin kotu akan sanya hijab din wanda ya kyale mata musulmai su sanya. Aregbesola ya kuma kara da bada shawarar cewa duk wanda bai gamsu da hukuncin kotun ba to ya nemi mafita ta hanyar shari'a.

"Shi dai bangaren shari'a sashe ne mai zaman kansa kuma matakan su ba su da alaka da na mu." In ji gwamnan.

"Hasalima abun dariya idan naji wasu na cewa wai gwamnati tana da sa hannu cikin shari'ar"

Aregbesolan kuma ya bayyana cewa ba aikin gwamnati bane kokarin jan hankalin mabiyanta zuwa wani addini wannan aikin iyaye ne da sauran masu ruwa da tsaki na al'umma. Daga karshe kuma gwamnan yayi kira ga iyaye da malamai da su taimaka wa gwamnati wurin yi wa yara masu tasowa tarbiyya ta gari domin samun ci gaba mai anfani cikin al'umma ba wai a a rika sa su cikin harkar siyasa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel