Zata iya shafar kowa idan aka cigba da kisan addini - CAN

Zata iya shafar kowa idan aka cigba da kisan addini - CAN

- An gargadin gwamnonin arewa da cewar kowa fa zata iya shafa idan dai har aka cigaba da kashe-kashen addini a kasar nan.

- Kungiyar kiristocin kudu maso gabashin kasar nan ne dai suka yi wannan gargadin bayan wani taro.

- Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kungiyar ta kiristoci tayi tir da kuma kakkausar suka a kan kisan da ake yima kiristoci a arewacin kasar nan.

Bayan taron nasu dai kungiyar ta kiristocin sun ce: "ta yaya za'a rika daukar yan uwan mu kamar awaki ko shanu ana kashe su haka kawai ba dalili bayan kuma ana ikirarin kasar nan ba ruwan ta da addini"?

Zata iya shafar kowa idan aka cigba da kisan addini -CAN

Rev. Samson Olasupo Adeniyi Ayokunle

KU KARANTA: Amaechi yayi magana kan faifan muryar sa yana sukar Buhari

"Wannan kwata-kwata bai dace ba kuma bai kamata ba don kuwa yana barazana ne da zaman mu kasa guda" suka kara cewa.

Bayan taron dai shugaban kungiyar Rev David Eberechukwu, tare da sakaten sa Apostle Dr Joseph Ajujungwa sun sanyawa takardar bayan taron hannu a inda suka kira gwamnonin arewacin kasar da su kare rayuka da kuma dukiyoyin al'ummar yankin.

"Kisan da akayi ma Mrs Bridget a kano da kuma kokarin kisan Emmanuel a Kaduna dole ne su zama na farko kuma na karshe indai ana son zaman lafiya cikin kasar".

Sanarwar ta kara da cewa musulman dake a kudancin kasar ya kamata su fada ma mutanen su na arewaci da su dena kashe kashen nan don suma su zauna lafiya. A wani labari kuma mai kama da wannan a jiya talata ne akwa kwashi yan kallo yayin da wasu dalibai kiristoci suka je makarantar boko da kayan coci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel