An kuma samun karancin man petir a Najeriya

An kuma samun karancin man petir a Najeriya

-karancin man petir ya dawo a kasar, yayinda mammalakin wani babban gidan mai yayi barazanar rufe gidan man

 

-Ibe Kachikwu, minista mai kula da harkokin mai, ya ba da umarni cewa, dukkan tashoshin sayar da man fetur, da su sayar da ko wani lita daya, tsakanin wannan farashin, N130.00, N135.00, N140.00.

An kuma samun karancin man petir a Najeriya
Ministan Mai Ibe Kachikwu

Mammalakin manyan tashoshin man petir a fadin kasar, ya yi barazanar dakatar da aiki, kan zargin shirin da ma'aikatar Nigeria National Petroleum Company (NNPC), ke yi na tsawwala masu a kan rage farashin man petur.

A cewar jaridar Vanguard, kungiyar Mega Filling Station Owners of Nijeria (AMFSON)  a jawabinsu a jihar Kaduna, sun da'awa cewa Ibe Kachukwu manajan darakta na kungiyar NNPC, ya bukaci manyan tashoshin man petir da su siyar da  mai a tsakanin  farashi N130.00, N135.00, N140.00, kan ko wani lita, alhalin kuma abokanan gasar su na siyar da ko wani lita a kan N145.00.

 

KU KARANTA KUMA: Sarrafa tattalin arziki

A halin yanzu, an fara fuskantar karancin mai a jihar River da jihar Bayelsa, yayinda kungiyar Nigerian Union of Petroleum and Natural Gas Workers (NUPENG) suka umurci masu gidajen mai da su rufe aiki, su shiga cikin yajin aikin da ke gudana.

An kuma samun karancin man petir a Najeriya

A halin yanzu, kungiyar NUPENG sun tafi yajin aiki a yankunan, wanda wasu kungiyoyi hudu a jihar River da Bayelsa suka ki goyon bayan hukuncin NUPENG. kungiyoyin sun hada da : Hilong Engineering Nigeria Limited, Uniterm Nigeria Limited, Specialist Drilling Fluid Nigeria LImited, da kuma Fudro Nigeria Limited.

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel