Kungiyar CAN ta samu sabon shugaba.

Kungiyar CAN ta samu sabon shugaba.

-Kungiyar mabiya addinin Krista a Najeriya CAN ta samun sabon shugaba biyo bayan zaben ta na kasa data kammala. Kungiyan Wanda take da hurumin jagorancin dukkan kungiyoyin mabiya addinin Krista guda 5 dake Najeriya ta kammala zabenta ainda  Rev Samson Olasupo Adeniyi na darikan baptist ya zama zakaran zaben..

Kungiyar CAN ta samu sabon shugaba.
Rev. Samson Olasupo Adeniyi Ayokunle

Kungiyar Kiristocin na cigaba da fusknatar rikicin shugabanci inda wasu ke ganin cewa tsohon Shugaba Oristejafor ya zama dan siyasa kuma yana ci da siyasa. Wannan ya zo ne bayan kalubale da yake cigaba da fuskanta daga wasu yan kungiyar da kuma wasu shugabannin cocin.

Anyi kokarin a sasanta rikicin ta cikin gida amma abun bai ci tura ba. Yanzu dai ana tsammanin zama domin manyan Fastocin su shawo kan matsalar shugabanci da kungiyar take ciki da kuma samun sahihin shugaba guda Daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel