Amaechi da Kachikwu sun samu sabani a cikin jama’a

Amaechi da Kachikwu sun samu sabani a cikin jama’a

- Ministan sufuri da karamin ministan mai sun samu sabani a bisa canja muhallin jami’an maritime da ke yankin neja delta

- Karamin Ministan mai Ibe Kachikwu na tuhumtar Rotimi Amaechi da nufin zama cikas ga cigaban yankin ta neja delta

Ministan sufuri Chibuike Rotimi Amaechi da karamin ministan mai John Ibe Kachikwu sun samu sabani a cikin jama’a akan canja muhallin jami’an maritime da ke ,okorenkoko,a jihar delta.

Yan siyasan biyu sun yi musun ne a wata farfajiyar ganawa a birnin Uyo ,babban birnin jihar Akwa ibom.

Ku karanta:

Amaechi da Kachikwu sun samu sabani a cikin jama’a
Dr. Ibe kachikwu, karamin ministan mai na jawabi

Shi Ministan sufurin ,Rotimi Amaechi yace gina jami’an bazata yiwu ba,amma a lokacin karamin ministan mai, Ibe Kachikwu ya hau mimbari yace :

“Gaskiya ban yarda da maganan ministan sufuri ba, duk ginin da za’ayi a yankin kudu ,mu yi hadun guiwa wajen karfafa shi,ba ruwan da zancen a tsawwala kudin filin, ba ruwana da ko nawa za’a saya filin, ko miliyan 19 ko 10,wannan ba ruwana bane.”

“Kudin filin bai shafi cigaban ginin ba. Ni abun da na sani ,an rigaya da  fara kasha kudi akan aiki, gaskiya ba za’a daina aikin ba

“Duk abin da aka kawo domin cigabn neja delta,zan karfafa shi, idan amaechi ya ki a gina ta a matsayin jami’an maritime, ni zan gina shi a matsayi jami’an mai.

“Kuma bisa ga maganan yin sulhu da ‘yan bindigan neja delta, inada bambancin ra’ayi da shi, ni ban taba gani ba, ko ina a duniya da aka samu zaman lafiya ta hanyar  yaki.

Kafin yanzu,Amaechi ya gana kwamitin majalisar dattawa akan sufurin ruwa akan canja muhallin jami’an.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel