Shugabanni Ibo sun yi kira da Buhari ya canza tsarin Najeriya

Shugabanni Ibo sun yi kira da Buhari ya canza tsarin Najeriya

Tsohon mataimakin shugaban kasar nan a jamhuriya ta biyu Cif Alex Ekwueme da tsohon gwamnan jihar Anambra Chukwuemeka Ezeife da kuma jigon tsohuwar jam'iyyar NADECO Ayo Adebanjo duka sunyi kira da shugaba Muhammadu Buhari da ya sake taswirar kasar nan zuwa na tarayya. Sunyi wannan kiran ne a yayin wani taro na 17 da kungirar Igbo Youths Movement a garin Enugu.

Shugabanni Ibo sun yi kira da Buhari ya canza tsarin Najeriya

Taron kuma ya samu halartar tsohon ministan yada labarai Jerry Gana, tshohon gwamnan jihar Anambara Peter Obi da Arthur Nwanko da kuma babban mai fafututa a yankin Neja Delta Ms Annkio Briggs.

KU KARANTA: Babban bankin Najeriya zaya takaita irin kudaden da za'a iya fitarwa

Mahalarta taron dai sun tattauna ne a kan yadda za'a maida kasar kan turba ta tarayya ta gaskiya a inda suka bayyana cewar idan har gwamnatin tarayya tayi hakan to tabbas za'a samu ragowar tashe-tashen hankula da kuma zanga-zangar neman raba kasar zasu ragu da fiye da rabi.

Shikau Cif Ekwueme ya kara da cewar tsarin da turawan mulkin mallaka suka bar Najeriya a kai shine bangarori ma su cin gashin kansu bawai jihohin da suka dogara da gwamnatin tarayya ba. Shima dai Adebanjo yayi kira da a koma ga tsarin asali da aka dora Najeriyar a kai domin samun zaman lafiya daga tsagerun Neja Delta da kuma masu son kafa kasar Biafara.

Shi kuwa tsohon minista Gana cewa yayi magabatan mu sunyi gaskiya da suka fara dora kasar bisa tafarkin tarayya inda yace wannan tsarin shine kawai yafi dacewa da kasar nan. Ya kuma nuna damuwar sa ganin yadda ake raba arzikin kasar nan inda gwamnatin tarayya ke daukar kaso mafi tsoka sannan a rarraba ma jihohi da kananan hukumomi sauran.

Gana ya kuma yi kira da shugaba Buhari ya duba kundin da taron kasar da akayi 2014 ya gaba tar ma tsohon shugaba Jonathan domin yin aiki da shi.

Ita ma dai Briggs wadda ta anshi lambar yabo a taron ta bayyanan cewar dole ne a maida kasar bisa tsarin Tarayya na gaskiya. Sannan ta kara da cewa duk da dai ta yadda zamu iya ci gaba ba tare da raba kasar ba idan dai har za'a koma tsohon tsarin tarrayyar amma idan ba a koma ba to tabbar ba za'a iya kaucewa rabuwar kasar ba.

Source: Legit

Mailfire view pixel