EFCC ta kwace gidan tsohon gwamna

EFCC ta kwace gidan tsohon gwamna

-Jami’an EFCC sun kama wani gida mallakin tsohon gwamnan jihar Adamawa, Umar Fintiri

-Gidan wanda ke Abuja an ce ya kai kimanin naira miliyan 500

-Hukumar ta kama tsohon gwamnan ne bayan bin wani takarda da ya ci kudi naira biliyan N1.9 lokacin da ya ke matsayin gwamna

-Finitiri yayi matsayin gwamnan jihar Adamawa daga 15 ga watan Yuli a shekara ta 2014 zuwa 8 ga watan Oktoba a shekara ta 2014

EFCC ta kwace gidan tsohon gwamna

Ibrahim Magu

Hukumar Economic and Financial Crimes Commision (EFCC), ta kama wani gida mallakin tsohon gwamnan jihar Adamawa, Umaru Fintiri.

A cewar jaridar The Punch, gidan da ke a No. 7, Gana street, Maitama, Abuja ya kai kimanin naira miliyan 500. Fintiri, wadda ya kasance kakakin majalisar na jihar Adamawa, ya zama gwamna bayan an tsige ainayin gwamnan, Murtala Nyako, da mataimakin sa, Bala Ngilari, a shekara ta 2014.

Hukumar EFCC, ta kama Tsohon gwamnan kwanaki 10 da suka wuce, bayan bin wani takarda daga tsofafin yan majalisar sa cewa, ya ci wasu kudi kimanin naira biliyan N1.9, a watanni 3 da yayi a matsayin gwamna.

KU KARANTA KUMA:  Masu fasadi na ci gaba da yaki da Sheriff- Bwala

Wata majiya a hukumar EFCC, ya ce ana zargin Fintiri da karkatar da asusun da aka nufa domin gida Faculty of Law a jami’ar jihar Adamawa.

Ya ce: “kafin tsigewar shi, Nyako ya bar ragowan naira N1,957,045,82 a asusun kwangila na gwamnatin jihar, tare da bankin Zenith Bank, reshen Yola, da namban asusu me 1011325467. Cikin kudin, naira miliyan N497 ya kasance na gina faculty na law a Jami’ar, wanda ya kamata ya zama a cikin tsohon kwalejin malamai, a  Yola."                                                                                                                                                      “Duk da haka, Lokacin da Fintiri ya ci gaba a matsayin gwamna, ya mayar da wannan faculty daga Yola zuwa harabar Mubi  na ADSU kuma daga baya ya aza harsashin gini, amma bayan wannan, ba’a ci gaba da kwangilar ba.”

Hukumar EFCC, na kuma binciken, naira biliyan N5 da Fintiri ya dauka a matsayin aro, lokacin da yake matsayin gwamna. Ana zargin cewa ya dauki bashin ba bisa ka’ida ba.

Duk da haka, wani mai Magana da yawun Fintiri, ya ce wai zargin bai inganta ba, ya kara da cewa dukkan kwangilar da aka bayar yayi daidai da  dokokin jihar. Ya ce ba’a kama gidan Fintiri ba amma  an sanya a karkashin bincike.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel