Jama'a sun taya iyalan Keshi bakin ciki

Jama'a sun taya iyalan Keshi bakin ciki

-Iyalan gidan Stephen Keshi a jihar Edo sunga ambaliyan masu juyayi

 -An ga Magoya baya, abokai, yan wasa, ex-internationals, sun cika a gurin ta'aziya

-Keshi, tsohon koci na Super Eagles ya mutu a ranar Laraba a birnin Benin

Jama'a sun taya iyalan Keshi bakin ciki

Bayan sama da sa'oi 48 da mutuwan tsohon kocin Super Eagles, Stephen Keshi, abokai, yan wasa, ex-internationals da magoya baya sun ci gaba da kai ziyara gidan marigayin dan mika ta'aziyarsu.

 Mutane sun kewaye babban birnin jihar Edo, dan taya iyalan marigayi  bakin ciki, ya rasu a ranar Laraba 8 ga watan Yuni, bayan an garzaya da shi zuwa asibiti dake kusa da gidan shi da ke GRA, Benin.

KU KARANTA: Fasto yayi Allah wadai da harin da aka kaima Francis Emmanuel

Ka tuna cewa, matar marigayi ta rasu sakamakon ciwon daji (cancer) a watan Disamba a shekara ta 2015, amma mutuwar Keshi ya zo wa mutane da dama a bazata.

Jami'an kungiyar NFF karkashin jagorancin Amaju Pinnik sun kai ziyara zuwa gidan tsohon kocin Super Eagles, a ranar Alamis, 9 ga watan Yuni.

 

Source: Legit.ng

Online view pixel