Masu fasadi da Sheriff

Masu fasadi da Sheriff

-Ali Modu Sheriff yace rahotanni da akayi na cewa hukumar EFCC sun kai farmaki gidan sa karya ne

-A cewar kakakinsa, Inuwa Bwala, aikin masu fasadi ne

-Ya ce masu Fasadin na bin son zuciyansu ne akan siyasa

Ali Modu Sheriff, shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party(PDP) da aka kora ya karyata jita-jitan cewa Hukumar Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) sun kai farmaki gidan sa a yammacin ranar Alamis.

Masu fasadi da Sheriff

 

Da yake jawabi ga Daily Post, Inuwa Bwala, kakakin Sheriff, yace jita-jitan aikin wasu masu fasadi ne wadda basa son su daina yaki da Shariff.

"wannan aikin wasu yan siyasa ne wadanda suke yakan Shariff, kuma suke son yin labari na qage a jaridu kamar yadda suka saba, amma ba abun damuwa bane, musamman mutanan jihar Borno.

KU KARANTA: Yadda Abba Moro ya yaudari mutane

Bwala ya ce ya shi bashi da masaniya akan kai farmaki gidajen Shariff na Abuja da jihar Maiduguri.

A cewar shi, lokaci na karshe da hukumar EFCC ta gayyaci tsohon Chiyaman din, ya girmama gayyatan kuma basu same shi da aikata ko wani laifi ba.

Ya ce suna da karfin gwiwan da zasu karyata yan fasadin yayin da zasu ci gaba da bin hanyar adalci da gaskiya.

Mataimakin chiyaman din jam'iyyar na kasa, Uche Secondus wadda yake kula da jam'iyyar, ya mika shugabancin ga Sheriff. Amma da yawa basu goyi bayan Shariff a matsayin Chiyaman ba suka kuma bukaci yayi marabus.

Jam'iyyar a wani zama ta kasa, a ranar 21 ga watan Mayu, sun kori Shariff a matsayin Chiyaman suka kuma daura Ahmed Makarfi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel