Osinbajo da Jonathan sun nuna jimami ga mutuwan Keshi

Osinbajo da Jonathan sun nuna jimami ga mutuwan Keshi

Yemi Osinbajo, Mataimakin shugaban kasan Najeriya, ya ce labarin mutuwan Stephen Kashi ya sa al’umma bakin ciki.

Osinbajo da Jonathan sun nuna jimami ga mutuwan Keshi
Mataimakin shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osibanjo

Keshi tsohon kyaftin kuma kocin na Super Eagle, ya mutu a ranar Laraba, 8 ga watan Yuni, bayan ya sha wahala a kamun da akayi masa. Mataimakin shugaban kasa ya ce yayi aiki mai girma tare matasa da senior national team da kuma hade kan kasa da kawo farin ciki ga mutane da yawa.

Har ila yau, maida martini ga mutuwar Keshi, tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana tsohon Kocin a matsayin adali,babban mai kishin kasa, kuma mafi cancantan jakada ga Najeriya. Jonathan ya bayyana marigayi dan kwalon kafa a matsayin wadda ya kawo daukaka da daraja ga kasar sa.

A halin yanzu, Solomon Dalung, Ministan Youth and Sport Development, ya nuna jimami da bakin ciki akan mutuwar Keshi, rahoto daga Channels TV. Yace labarin mutuwan yazo masa a ba zata, tunda ba wai tsohon kocin yayi rashin lafiya bane kafin mutuwar sa. Ministan wasan ya tabbatar way an Najeriya  cewa gwamnati zata nemi hanyoyi da za’a tunga tunawa da marigayin.

Yace: “yana da nauyi a azuciya, amma godiya ya tabbata ga Allah Madaukaki, a madadin ma’aikatan matasa da wasanni da kuma gwamnatin tarayya na Najeriya, ina nunu juyayi tare da iyali na Coach Stephen Okechukwu Keshi(MON) da kuma dukkan yan kwalon kafa na Najeriya akan rasuwar mai kwazo da kuma gwarzo da yayi fice."

Dalung ya bayyana Keshi a matsayin daya daga cikin gwarzayen Najeriya da suka taimaka gurin ci gaban kwalon kafa da wasanni a Najeriya. Keshi ya zama koci a Nigeria National Team a shekara ta 2011 kuma shi  daya ne kocin Najeriya da ya taba cin Africa Cup of Nations.

Asali: Legit.ng

Online view pixel