Ana mulkin Najeriya kara zube babu tsari - PDP

Ana mulkin Najeriya kara zube babu tsari - PDP

Jamiyyar adawa ta PDP ta bayyana cewar ana mulkin kasar nan ne kara zube kawai tun bayan saukar su a kan mulkin kasar 29 ga watan Mayun bara. Jam'iyyar ta kara da fadar cewa wasu yan tsiraru ne kawar karkashin Mamman Daura suke juya kasar yadda suke so.

Ana mulkin Najeriya kara zube babu tsari - PDP
Mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP

Jam'iyyar ta kara da cewa babu abunda gwamnatin nan ta tsinana ma yan Najeriya sai dai hutuna a inda suka kara da cewa hutunan ne kawai za'a cigaba da yi har zabe ya sake zagayo wa.

A hannu daya kuma wata kungiya mai fafutukar ganin jam'iyyar ta din ke barakar ta sun yi kira da dukkan sassan jam'iyyar da su mai da wukaken su sannan kuma su rungumi sulhu tare da yin mubaiya ga shugaban rikon kwaryar jam'iyyar Ahmad Makarfi.

Shugaban kungiyar mai suna Adamu Gebriel ne ya yi wannan kiran a garin fatakwal din Jihar Rivers.

Asali: Legit.ng

Online view pixel