Gwamnatin ingila tayi Magana akan nufin zuwan Buhari

Gwamnatin ingila tayi Magana akan nufin zuwan Buhari

- Jita-jita za fara tasowa cewan manufar shugaban kasa muhammadu buhari na zuwa landan dama kan zancen tsagerun neja delta ne

- Gwamnatin kasar injila ba tada masaniya game hakan

 

 

Gwamnatin ingila tayi Magana akan nufin zuwan Buhari

Gwamnatin kasar ingila ta fito tayi Magana akan rahotannin da ke cewa shugaban kasa muhammadu buhari dama ya je birnin landan ne domin ganawa da tsohon shugaban kasa goodluck janathan akan tarzoman neja delta

KU KARANTA: Sojin Najeriya ta jaddada tsagaita wuta na mako 2

A wani jawabin da kakakin offishin jakadan ingila da ke Abuja, joe abuku  ya gabatar, ta karyata wannan jita jitan, ya sake nanata cewan buhari ya je landan ne domin  ciwon kunnensa.

“ Rahotannin kafafun yada labarai  da ke fadin cewa gwamnatin injila ta shirya wata ganawa tsakanin shugaban kasa buhari,tsohon shugban kasa goodluck jonathan,da wasu wakilan kungiyoyin neja delta domin tattaunawa akan tarzoman dake faruwa karya ne,” jawabin yace.

" Muna sane da cewan shugaban kasa na landan a yanzu neman sauki. ba mu da wata masaniya akan ganawa da wasu tsagerun neja delta"

Rahotannin sun taso ne a ranar laraba,8 ga watan yuni cewa akwai yiwuwan shugaba buhari zai zauna da tsagerun neja delta a landan. An zarge gwamnatin ingila ne da cewa tana yunkurin shirya sulhu tsakanin najeriya da tsagerun neja delta. Buhari ya bar kasan ne ranar 6 ga watan yuni domin ya huta kuma ana sa ran dawowansa  ranar alhamis 16 ga watan yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel