IPOB tayi kuli kulin kubura da tayin Obiano

IPOB tayi kuli kulin kubura da tayin Obiano

- IPOB ta zargi Gwamna Obiano na kokarin samun shahara a sama

-  kungiyar tace shi bata bukatar  tayin gwamnan

- wani jigon APC a Enugu kuma ya zargi gwamnan

IPOB tayi kuli kulin kubura da tayin Obiano
IPOB members at a rally

Asalin mutanen Biyafara (IPOB) sunyi jefi da tayin da Gwamna Wille Obiano na jihar Anambra yayi na yunkurin biyan takardardun  kudi asibitin ‘yan tsẽgumin Biyafara dasu ka ji rauni a bikin zagayowar yakin biyafar shekaru arbai’in da tara.

KU KARANTA: Har yanzu ba'a biya matasa kudin su ba.

Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa gwamnan ya yi alƙawari a zauren ganawar garin Nkpor  da ya jẽ nuna juyayi tare da mutanen Nkpor. A lokacin bikin yin shellar Biyafara a ranar Litinin, 30 ga watan Yuni, an samu wata mumunan karo tsakanin ‘yan tsẽgumin Biyafara da sojoji, wanda da ya kai ga mutuwar wasu ’yan kungiyar kuma da dama sun samu rauni.

IPOB ta hanyar kakakin kungiyar, Mr Emma tayi kuli kulin kubura da  tayin da gwamnan yayi na biyan diyyan takardardun kudin asibiti na raunin da ‘yan Biyafara da kuma wadanda ba  ‘yan Biyafara suka ji,sun bayyana cewa wannan kuka ce bayan mutuwa.

"Gwamnan na zagin iyalan matattun ‘yan Biyafara da kuma waɗanda suke jinyan raunuka harbin bindiga daban-daban a asibitoci, kuma ma ku sani, babu mai rauni harbin bindigan da ke a jihar Anambra yanzu, duk mun fitar da su daka jihar saboda sojoji na bin asibitoci dan nemansu. "

Chief Zeribe Ezeanuna da wanda yake  jigo na APC a jihar ya bawa gwamnan laifin faruwar hayaniyar. Ya bukace shi da yayi wa kansa uzuri saboda ba zai yiwu sojoji su buda wuta ba in ba da izininsa ba,

A halin yanzu, IPOB ta lakabawa  dattawan igbo da suka ziyarci shugaban kasar Muhammadu Buhari a matsayin yan cin amana. Dattawan sun  ziyarci shugaban kasa a cikin farkawa daga cikin karo da ya faru tsakanin masu zanga-zanga da kuma ‘yan tsẽgumin Biyafara.

A cikin wata sanarwa dauke da sanya hannun mai gudanarwanta, Clifford Iroanya, kungiyar ta ce ta yi mamakin irin waɗanda suka garzaya zuwa wurin Buhari domin taya shi murnar kashe yan  Biyafara a rana irin ta wannan a maimakon yin Allah tir da kuma yunkurin dawo da Biyafara.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel