Najeriya Zata Shawo Kan Matsalolin Ta Inji Wani Fasto

Najeriya Zata Shawo Kan Matsalolin Ta Inji Wani Fasto

Shuugaban majami'un Deeper Life Bible Fasto William Kumuyi yace yan Najeriya zasu kada su karaya don kuwa matsalalin tsaro da tattalin arzikin da ake fama dashi a kasar nan zai zama tarihi nan ba da dadewa.

Najeriya Zata Shawo Kan Matsalolin Ta Inji Wani Fasto

Shahararren Faston ya kara da cewa kasar nan zata farfado sannan kuma tayi cigan da yafi na da. A bangare daya kuma yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta zauna teburin sulhu da tsagerun Niger Delta da nufin kawo karshen tashe-tashen hankuna a yankin.

KU KARANTA:  Manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Talata

A cewar Faston sai kowa ya bada gudummuwar sa ne ta hanyar yakar bambance-bambance sannan ne kasar nan zata cigaba. Faston ya kara da cewa "kamata yayi mu maida hankalin mu kacokan wajen cigaban kasar nan ba wai kullum tunani ya za'ayi a raba ta ba sannan kuma dole ne sai an rika hakuri tare da yin sulhu". A wani labari kuma mai kama da wannan gwamnatin Najeriya ta bada umurnin janye sojoji daga yankin Naija Deltan jin kadan bayan taron da Shugaba Buhari yayi da shugabannin yankin.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel