Sojin ruwan Najeriya sun kama wani mai fasa Bututun mai a Neja Delta

Sojin ruwan Najeriya sun kama wani mai fasa Bututun mai a Neja Delta

Rundunar sojin Ruwan Najeriya ta bayyana ma manema labarai cewar sun kama wani babban mai fasa bututun mai a yankin Naija Delta a Jihar Delta.

Sojin Ruwan Najeriya Sunkama Wani Mai Fasa Bututun

Sudai tsagerun na Naija Delta sun sha alwashin ci gaba da kai hare-hare a kan bututun mai da gas din da ke a yankin nasu duk kuwa da girke sojojin Najeriya da akayi a yankin.

Shugaban na masu fasa bututun dai ai bayyana ma manema labarai shine a garin warri dake Jihar Delta ranar litinin tare da wasu wadan da ake tuhumar kan aikata laifuka da dama ciki hadda kisan da akayi wa wani jami'in tsaro da mutane gari a kauyen Batan din Karamar hukumar Warri ta kudu maso Yamma a ranar 30 ga watan Aprilu.

A jawabin shugaban sojin da yayi ma manema labaran Commodore Raimi Muhammed yace kama babban mai basa bututun nasara ce babba da zata takaita kai sabbin hare-haren a yankin.

Shugaban sojin ruwan kuma ya kara da cewa an kwato makamai da dama daga hannun wadanda aka kama din. A wani labari kuma kasar Amuruka ta yi kira da dukkanin bangarorin su zauna bisa teburin sulhu domin sasantawa da kuma kawo zaman lafiya mai dorewa a yankin da kuma kasa baki daya.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel