Manyan Labarai 10 Da Suka yi Fice Jiya Litinin

Manyan Labarai 10 Da Suka yi Fice Jiya Litinin

Ma'aikatan Kamfanin Legit.ng sun zakulo maku masu karatu labarai fitattau wadan da suka fi shahara jiya litinin 6 ga watan Juni. Gasu nan:

1. Abin Al'ajabi: Majalisar dinkin duniya ta bada shawara da a raba Najeriya zuwa yankuna shidda (6).

Wasu masu goyon bayan kafuwar kasar Biafara a majalisar dinkin duniya sun bada shawarar cewa yakamata a raba Najeriya zuwa gida shidda. Suma kuma masu fafutukar ganin a kafa kasar ta Biafara sun yi na'am da wannan shawarar.

2. Shugaba Buhari Ya Tafi Birnin Landan domin jinyyar ciwon kunne da yake fama dashi.

Shugaba Buharin dai ya tashi ne zuwa birnin Landan din a Jiya litinin daga filin sauka da tashi na kasa-da-kasa dake Abuja.

3. Likitocin Kasashe Renon Ingila sunyi Tofin Allah Tsine game da tafiyar Shugaba Buhari yayi Birtaniya domin Jinyar ciwon kunnen sa.

Dr. Enabulele Osahon wanda shine mataimakin shugaban kungiyar likitoci renon Ingila ne ya bayyana rashin jin dadin su game da tafiyar ta shugaban.

Sannan kuma ya kara da cewa Najeriya tana da kwararrun likitocin Kunne har 250 da kuma cibiyar bincike na kunne dungurun gum dake Kaduna amma duk da hakan shugaba Buhari sai ya tsallake su ya tafi waje.

4. Babbar Magana: Tsagerun Naija-Delta Sun Sha Alwashin Kona Fadar Shugaban Kasa, Hedikwatar Yan sanda, Babbab Bankin Najeriya Da kuma Hedikwatar Sojojin Kasa.

A jiya litinin ne wasu tsagerun Niger Delta watau -Joint Niger Delta Liberation Force (JNDLF) -suka fitar da sanarwar zasu Kona Fadar Shugaban Kasa, Hedikwatar Yan sanda, Babbab Bankin Najeriya Da kuma Hedikwatar Sojojin Kasa.

5. Wani Dattijon Arewa Ya cewa Yan Nijer Delta Su je su sha Mansu.

Sanata Joseph Kennedy N Waku wanda kuma jigo ne na kungiyar dattawan arewa watau Arewa Consultative Forum ya yima tsagerun Nija Delta wata magana mai kama da habaici a inda ya ce suje su sha man da suke takama da shi mukuma a cewar shi "sai mu rike kayan noman mu".

6. Wani Fasto Ya Bayyana Dalilin da yasa Gwamnatin Buhari Ta kasa Abin Kirki Har Yanzu

Fasto Enoch Adeboye wanda kuma shine shugaban rukunin coci-cocin Redeemed Christian Church Of God (RCCG) ya ce dalilin da yasa gwamnatin Shugaba Buhari ta kasa tsinana wani abun kirki bai wuce rashin koma ma Allah da basuyi ba.

7. Sojin Ruwan Najeriya Sun Dakatar Da Mamayar Da sukayi ma Kauyen Oporoza

Sojin ruwan Najeriya sun kawo karshen mamayar da suka yima kauyen Oporoza dake cikin karamar hukumar Warri ta Kudu maso Yamma dake Jihar Delta bayan kwanaki ukku da sukayi.

8. Tsohon Shugaba Jonathan Ya bayyana Dalilan Da yasa Ake Bincikar sa

Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Goodluck Jonathan wanda shine ya lashe kyautar gwarzon Shekara na wata babbar jaridar yan afrika a kasar Amuruka watau The African Sun Times ya bayyana cewar zargin cin hanci da rashawar da gwamnatin Shugaba Buhari keyi masa ne dalilin da yasa ake bincikar sa.

9. Akwai Yiwuwar Shugaba Buhari ya kara tsawon hutun da ya dauka sakamakon wata rashin lafiyar daban

Alamu na nuna cewar akwai yiwuwar shugaba Buhari ya kara tsawon hutun da ya dauka na kwana goma na jinyya sakamakon wata cutar da ke shirin bullowa kuma.

10. Hoto: Dan Abacha Ya samu Karuwa

Matar Dan tsohon shugaban Najeriya General Muhammadu Abacha Hamama ta samu karuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel