NFF tana zage danste akan tikitin ta rasha 2018 – pinnick

NFF tana zage danste akan tikitin ta rasha 2018 – pinnick

Pinnick na tabbatar da cewa gwamnatin sa na zage danste wajan hayewar su gasar kwallon kafan ta duniya

NFF tana zage danste akan tikitin ta rasha 2018 – pinnick

Shugaban ta NFF ya bayyanawa manema labarai a offishin sa dake gidan glashi a ranar litinin,shida ga watar yuni. Pinnick na bada tabbacin cewa,ko shakka babu,sai fa sun je kasar rasha 2018

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta najeriya(NFF), Amaju Melvin pinnick yana jaddada cewa yana nan yana bada goyon bayansa da karfin guiwa domin tabbatar da cewa ‘yan kwallon kafan mu sun haye gasar kwallon kafa ta duniyar da za’ayi a kasar rasha 2018.

Bayan ya amincewa gazawarsu na hayewa gasar kofin ta nahiyar afrika ta shekaran 2017( sau biyu a jere), yace abin ban takaici ne,amma yana tabbatar da cewa,zuwa kasar rasha ta zama dole.

Ya ce: “ba zamu yarda komai ya Dauke mana hankali ba,daga ko ina, muna nan da niyyan zuwa rasha,kuma sai munje. Abinda ya kawoni offis kenan yau. “mashawarta sunyi dubi ga abubuwa da dama don shiryawa cinken da za’ayi ranar ashirin da hudu ga watan yuni.”

Pinnick ya bayyanwa manema labarai a offishin sa da ke gidan gilashi,tare da manyan yan kwamitin NFF, su chris green,Ibrahim musa,sharif rabiu inuwa,Sunday dael-ajayi,babagana kalli da ahmad yusuf fresh.

Akwai su bola oyedode( direktan gasa), ademola olajirew( direktan labarai), tuned aderigbigbe( direktan abubuwan da suka shafi siyasa), chikelue lloenyosi (babban mai bada shawara akan tsaro), okey obi (babban lauyan su), da nasiru jibril( mataimakin sirri ga shugaban NFF).

Pinnick ya fadi karuwan da aka yi ,daga wasan kwallon abota da akayi da kasar mali da luzambog, yana cewa wasannin biyu na nuna shirin najeriya.

Shugaban na NFF,tareda babban sakataren, mouhammad sanusi da sauran mashawarta sunyi ganawa da juna daga baya.

Source: Legit

Online view pixel