Malamar makaranta ta saci tukunyan amala

Malamar makaranta ta saci tukunyan amala

Wata malamar makaranta a makarantar sakandare na Baptist a jihar ekiti ta saci tukunyan amala daga kicin din makwabciyarta saboda ba’a biya su albashi ba. Malamar ta kai abincin dakin ta ne domin ta ciyar da yaranta guda biyu amala da dayyen manja Ganin haka,Ita makwaciyar mai abincin saboda takaici da tausayi,ta je ta kawo musu miya domin suci su koshi. 

Wani abin al’ajabi ya faru ne a garin igede ekiti,hedkwatar karamar hukumar irepodun/ifelodun ta jihar ekiti a ranar lahadi,biyar ga watan yuni, yayin da wata malamar makaranta ta saci tukunya cike da garin doya wanda akafi sani da ‘amala’ daga wurin makwabciyar ta.

An ji Daga wani majiya dake zaune a anguwar cewa malamar makarantan dake aiki a makarantar sakandare na Baptist,ta saci tukuyan ne domin ciyar da yaranta guda biyu, jaridar Nation ta ruwayto.

Majiyar tace ”hakan ya faru ne a kimanin karfe daya da rabi ta ranar lahadi, yayinda ma’abota addinin kirista suka dawo daga coci, saboda ita malamar ta kasa zuwa cocin saboda yunwa bata da hankali.

“makwabciyar dawowanta ke da wuya,ta daura sanwan amala ,ashe malamar na ta biye biyen ta,da ta bar kicin din.

“barin kicin dinta ke da wuya, sai ta afka ta dauke tukunyar abincin ta kai dakin ta.

“ mai abincin tayi kuwa kuma abin ya bata tsoro da tayi ram da ita da yaranta guda biyu suna cin amalar da zallan manja.

“ saboda tausayi, makwabciyar ta koma dakinta ta kawo musu miya domin suci su koshi.”

Rahotanni sun nuna cewa ,da yawa daga cikin ma’aikatan jihar ekiti sun koma kauyikansu domin yin noma saboda rashin tabbacin cewa za’a biya su albashi.

Wata majiyar tace:” da yawa daga cikin abokan aiki na sun koma karkara domin cin wannan daminar, saboda in gemun dan uwanka ya kama da wuta,ka yayyafawa taka ruwa.

“kun san wannan yajin aikin ta samu cikin halin kakanikaye, kuma munga rayuwa tafi arha a karkara ,kuma mutane da dama na shuka yabanya kuma su girba cikin watannin uku.

“wadansunmu kuma,suna shuka kayayyakin masarufi saboda tabbatar da tsaro idan lokacin ritaya tayi.

“kuma na san wadansu da suka fara koyan sana’o’in hannu kamar dinki,daukan hoto,wanzanci,kwalliyar gida, da sauran su

“wadanda can dama suna hada kasuwanci da aikin gwamnati ,su ke jin dadi yanzu.”

Gwamna ayodele fayose ya fada wa ma’aikatan jihar tasa ta ekiti cewa su daina wannan yajin aikin fa domin a biyasu.

Ma’aikatan su fara yajin aikin ne a ranar alhamis ,ashirin da shida ga watan mayu, kuma faruwan hakan,ya sa duk offishoshi da makarantun gwamnati da ke birnin jihar ta ado ekiti a kulle har yanzu.

Amma, gwamna fayose ya sanar cewa wadannan matsanaciyar hali da suke ciki,ba jihar ekiti kadai ta shafa ba,saboda jihar ta dogara ne da kudin da gwamnatin tarayya ke bata.

An tara cewa, an biya albashin watan disamba na shekaran da ya gabata ne watar maris na wannan shekaran.

Asali: Legit.ng

Online view pixel