NPFL: Wikki Tourist sun daga zuwa sama

NPFL: Wikki Tourist sun daga zuwa sama

- An samu nasarori biyu a kwallon da aka buga a waje a ranar Lahadi a cigaba da gasar kwararru kwallon kafa na Najeriya watau (NPFL).

- Kakar wasan kwallon kafa na 2015/2016 wanda ya shiga mako na 20 a fadin kasar.

- Kungiyar kwallon kafa ta Enugu Rangers ta samu gagarumar nasara a Owerri a wasan da ta buga a filin wasa na Dan Anyim.

Ga rahotanni da kuma sakamakon fafatawar

NPFL: Wikki Tourist sun daga zuwa sama
Action during an NPFL game

Ba sai na fada be cewa kulop din Ikorodu United zai koma aji na biyu a rukunin kwallon kafa na Najeriya bayan da ya sha kashi a hannun Wikki Tourists.

Idris Guda tauraron Kulop din Wikki Tourists wanda ya jefa kwallo a raga, a minti 85 da soma wasan, ya tabbatar da nasarar kulop din a wasan da suka buga a waje.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun hallaka yan Boko Haram 11

Wannan nasara na nufin cewa Wikki Tourist su ne kan gaba a teburin gasar ta NPFL bayan sakamakon mako na 20.

LURA: Za ka samu labarun wasanni da dumi-duminsu a manhajar Naij sports

Kulop din Heartland 1, Kulop din Enugu Rangers 2

Dan wasa Chisom Egbuchulam wanda ya shigo a matsayin canji, shi ne ya ci kwallon da ta ba kulop din nasara a karawar da aka yi.

Kulop din Sunshine stars 1, Kulop din Abia Warriors 1

Kulop din Sunshine stars dai ya gaza samun nasara a wannan karawa da aka yi, duk da cewa kulop ya ci a arangamar da aka yi Umuahia a wasan farko.

Kano Pillars 1, Plateau United 0

Kano Pillars sun kammala wasannin su hudu ba tare da nasarar cin balabalai ba. Sai dai sun taki sa’a, a lokacin da suka ci Plateau United daya mai ban haushi a Kano, cin dan da kyar!

KYAUTA: Samu labaran wasanni da dumi-duminsa a manhajar Naij sports

Kulop din 3SC 3, kulop din Akwa United 0,

Mai horar da ‘yan wasa Gbenga Ogunbote ya dawo kulop din Shooting Stars na Ibadan da sa’a, ya yi nasarar jefa kwallaye 3 a ragar Akwa United wadanda suka kawo masu ziyara, kuma wadanda a da, su ke kan gaba a tebur.

Kulop din Niger Tornadoes 2, kulop din Ifeanyi Ubah 1

Ba don nasarar da ‘yan Niger Tornadoes suka samu akan Ifeanyi Ubah ba, da mai horar da ‘yan wasan Abdul Biffo ya shiga tsaka mai wuya. ‘Yan Tornadoes din sun fidda Kociyan nasu kunya a yayin da suka lallasa bakin da ci 2 da 1.

LURA: Za ka samu labaran wasanni da dumi-duminsu a manhajar Naij sports

Rivers United 1, Lobi Stars 0,

Nasarar da kulop din Rivers United ya samu akan Lobi na ci 1 mai ban haushi, da ya dora su akan teburin NPFL, amma nasarar da Wikki Tourists ta samu a Lagos ya bata lamarin ‘yan Fatakwal din.

Nassarawa United 2, Eyimba 1 Kulop din Nassarawa United sun taki babbar sa’a da suka lallasa Eyimba da ci 2, wanda hakan ya daga martabar kulop zuwa ci 8 wasannin da suka buga a gida, bayan sun kayar da zakarun a Makurdi

Asali: Legit.ng

Online view pixel