Sojojin Najeriya sun hallaka yan Boko Haram 11

Sojojin Najeriya sun hallaka yan Boko Haram 11

- Sojojin Najeriya sun ce sun rasa abokin aikin su guda daya a jiya Alhamis a yayin da suke fada da yan Bokoharam a jihar Bornon Najeriya.

- Mai magana da yawun rundunar sojojin ne dai watai Sani Usman ya bayyana hakan a wata sananrwa da ya fitar a jiyan

Sojojin Najeriya sun hallaka yan Boko Haram 11
Wasu yan ta'addan Boko Haram

Usman yace rundunar sojojin dake a bataliya ta 112 daga Mafa Zuwa Dikwa duk acikin jihar. Borno din ne yan ta'addan suka farmawa a wane kauye da ake cema Ajiri.

"Duk da dai sojojin sun samu nasarar korar yan'ta'addan amma dai sun rasa soja guda sannan kuma wasu guda 3 sun samu raunuka. Haka ma kuma mutum daya daga cikin sojojin sa kai watau JTF din shima ya samu rauni" a cewar shi.

KU KARANTA: Kungiyar Kwadago zata matsa ma Gwamnatocin Jihohi

Usman din kuma ya kara da cewa an dauke gawar sojan da kuma wadan da suka samu rauni zuwa asibitin sojoji dake a maiduguri. Sannan kuma ya kara da cewa yan ta'addan 8 ne suka rasa rayukan su a yayin ba-ta-kashin da akayi sannan kuma sojojin sun yi nasarar kwato. Makamai masu yawa daga hannun yan ta'addan.

Yace cikin makaman da aka kwato sun hada da bindugu da kuma harsasai da kuma boma-bomai guda uku. A wani labarin kuma an ruwaito cewar cututtuka sun farma yan ta'addan da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel