Dani Alves ya rubuta wasika a shirin Brain Bercelona

Dani Alves ya rubuta wasika a shirin Brain Bercelona

- Dan Alves na shirin barin Barcelona a wannan bazara

- Dan wasan zai koma Juventus

- Alves ya rubuta wasika mai Sosa rai

Dani Alves ya rubuta wasika a shirin Brain Bercelona
Yan wasan Barcelona

Tauraron kulop din Barcelona wanda ke shirin komawa Juventus a cikin bazara ya rubuta wata wasika mai Sosa rai ga kulop din. Daraktan wasanni na Barcelona Robert Fernandez ne ya tabbatar da barin mai bugun bayan kulop din zuwa Juventus a bazara wannan shekara.

Dan kasar Barazil din Wanda ya Sanya wani sharadi a kwantiraginsa na samun ya sarara zuwa wani wuri na wani lokaci, zai Kare ne a bazarar, ya kuma amince da wani kwantiragi na shekara 3 da Juventus.

KU KARANTA: Manyan mutane sun halarci wasan Holo na Kaduna

A nasa bangaren dan Shekarau 33 da haihuwa Alves, Wanda ya zo Barcelona a shekarata 2008, ya rubuta cewa: " Saura wata daya in cika shekara takwas a Barcelona. A watan Yuli na 2008 na zo wannan kulop din, kuma a karon farko na samu gurbi a dakin canza kaya na 'yan wasa a inda na dandana wani babban sauyi na cigaban sana'ata ta kwallon kafa.

Daga ranar farko a wajen karbar horo a karkashin Pep Guardiola zuwa kakar wasan na karshe, na yi arziki da jin dadin taka leda iron yadda na ke so.. Ba zan manta da lokutan da muka kasance tare da juna ba tun daga sansanin horo na Nu zuwa many an filayen wasa na duniya, da kuma kan titunan garin Barcelona.

Lokutan murna da farin cikin cin kwallaye gani da bukuwa, ababen alfahari ne da garin cikin a gare ni Wanda ba zan manta ba. Gaskiya na samu daukaka a kwallon kafa , kuma baiwa ta sa na samu alfarmar sa ka rigar days daga cikin manya -manyan kulop din duniya har tsawon wasu Shekaru, Savona ingancin 'yan wasan da kuma masu horar da su.

Zan iya kiran sunayen wadanda suka taimakawa zamana a nan, amma na gwammace in mika godiyata a jimlace saboda ko a dakin sa kaya na 'yan wasa ba'a maganar daidaiku, Sai dai a gudu tare a tsira tare.

Kama da shugabanin kulop din, zuwa masu horar da ' yan wasa da sauran masu hidima ina mika godiyata. Wannan wasika ba ta ban kwana bace, takarda ce ta sanar muku cewa zan matsa gaba domin neman karin daukaka a sana'ata. Na tafi amma zan dawo. Nagode da kaunar da ku ka nuna min". Barcelona suma sun godewa Alves a wata sanarwa da kulop don ya fitar.

Shugaban kulop din Joseph Bartomeu ya ba dan wasan amsa kamar haka: "Barcelona na mika godiya ga Dan Alves dangane da shekarun da yayi a tare da mu. A yayom zamansa, ya taimaka wajen ci gaban kulop din da kuma daga darajarsa."

Shugaban ya kuma kara da cewa: "Tun lokacin da ya zo daga Seville a 2008, ya zama Dan wasa daga kasar waje na biyu a yawan buga mata kwallo a inda ya ciwo mata kofuna 23." Bartomeu ya jadda cewa "mayar da hankali da kuma kirkin sa ya sa ya zama abin kaunar magoya bayanmu. Saboda wannan dalili ne ya sa za mu bukaci da ya yiwa magoya bayanmu sallama a farkon kamar wasanni mai zuwa. Barcelona na yi ni shi fatan alheri a Inda zai koma."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel