Hari ga soji: Niger delta avengers ta alwashi gano masu laifin

Hari ga soji: Niger delta avengers ta alwashi gano masu laifin

Kungiyar masu ramuwa ta neja-delta tayi Allah tirr da kisan runduwar sojojin najeriya a ejere,karamar hukumar warri ta kudu a jihar delta

Suna bawa iyalen sojojin da aka kashe tabbacin cewa sai ta gurfanar dasu

Hari ga soji: Niger delta avengers ta alwashi gano masu laifin
Tsagerun Nija Delta Avengers

Kungiyar ta masu ramuwa ta neja-delta na begen masu “masu fadar yancin kai” ta yankin da su koyi usulubinta na tabbatar da cewa ba rai mara haqqi na za’a rasa a wurin gudanarda hanzugansu. Tashar yada labarai ta Premium times ta ruwaito cewa kuygiyar yan ramuwar ta neja-delta ta mika sako wanda Mudoch Agbinibo ya sanya hannu a ranar alhamis ,biyu ga watar yanaya, tattare da tuhumar da akeyiwa kungiyar na kai hari wa jirgin ruwan sojojin najeriya a garin ejere ta karamar hukumar warri ta kudu a jihar delta.

KU KARANTA: Cif Ifeanyi Ubah ya kuduri sake tsayawa takara

Tana jaddadawa “kisan sojojin ba haqqi ba halinsu bane kuma ba usulubinsu bace”, kuygiyar yan ramuwar ta neja-delta tayi Allah tir da kowani hari akan sojoji da masu farin wula.

Suna cewa;

“Munyi alkawari wa duniya, a yunkurin kwato yancin mutanen mu, ba jinin sojan gwamnatin da za’a zubar komin zabin al’amari.

“Harda jinin azzaluman sojojin bazamu zubar ba,yakinmu akan kafufuwan man fetur ne ba rayukan mutane ba. Tunda bamu iya bada rai,to bamu da haqqin daukan rai . Amma muna sake tabattar wa iyalen sojojin da suka rasa rayukansu cewa sai mun gurfanar da wadanda suka aiwatar da kisan.

“idan lokacin batakashi da sojoji yayi ,duniya ta sani cewa bazamu fara kai hari ba.”

Kuygiyar ta yan ramuwa ta neja-delta na begen masu “masu fadar yancin kai” ta yankin da su koyi usulubinta na tabbatar da cewa ba rai mara haqqi na za’a rasa a wurin gudanarda hanzugansu.

”Wannan sakon tana nufin ko wani kungiya mai ikirarin fadan kwato yanci, zaku iya yaki dan yantar da mutanenku ba tare da kisan rayuka maras haqqi ba, mun saukar da sarrafa man feturin najeriya daga ganga miliyan biyu(2 million barrel) a rana zuwa ganga dubu dari takwas(800,000) kacal ba tare kisan rai daya ba, dan haka muna bada gargadi ga kowanne kungiya da a kwaikwayi usulubin mu,” suka ce.

Kuygiyar ta yan ramuwa ta neja-delta sun dau alhakin bama baman da suka shafi kafufuwar man fetur ta kamfanonin chevron,agip da NNPC,a kwanakin da suka gabata.

A jiya ko da daddare,sun kai hari ga bututun kamfanin Shell (SPDC) dake kusada forcados ,a jihar delta, da kuma wadansu bututu guda biyu a jihar bayelsa.

Bayan harin da suka kai, suna bada gargadin cewa sai sun tabbatar cewa sai sarrafa man najeriya ya sauko sifili.

Asali: Legit.ng

Online view pixel