Lauyoyi sun soki Obasanjo akan zagin Mai Shari'a

Lauyoyi sun soki Obasanjo akan zagin Mai Shari'a

-Tsohun Shugaban kasa Olusegun Obasanjo yazo karkashin akan zagin Justice Mohammed Idris na babban kotun tarayya a jihar Lagas

-Obasanjo ya bayyana mai shari’an a matsayin “Jahili kuma wawa” akan ya nemi dukkan shuwagaban farar hula daga shekara ta 1999 da su lissafa ganiman da aka dawo dasu daga gurin Sani Abacha

-Kolawole Olaniyan, mai ba da shawara ga kungiyar International Secretariat of Amnesty International a London, yace sukan Obasanjo bai zama hari ga masu shari’a kawai ba harda yancin yin bayanai

-Olaniyan ya bayyana hukuncin Justice Idris a matsayin “nasara mai girma akan nuna gaskiya a kasa”

Lauyoyi sun soki Obasanjo akan zagin Mai Shari'a
chief olusegun obasanjo

Kolawole Olaniyan, mai ba da shawara a International Secretariat of Amnesty International a London, ya soki tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo akan zagin Justice Mohammed Idris na babban kotun tarayya da Jihar Lagas.

KU KARANTA: Ngozi Okonjo Iweala ta bada jawabi a taron MIIT

Obasanjo ya bayyana mai shari’an a matsayin “Jahili kuma wawa” akan ya nemi dukkan shuwagaban farar hula daga shekara ta 1999 da su lissafa ganiman da aka dawo dasu daga gurin marigayi daraktan sojoji, Sani Abcha.

Bisa ga rohoto daga jaridar The Punch, mai shari’an ya bayar da umurni akan gwamnatin Obasanjo, Musa Yar’ Adua da kuma Goodluck Jonathan da su buga daki-dakin akan yanda aka kashe ganiman da aka nemo na Abacha

Maida martini akan ci gaban, Obasanjo ya nuna rashin yardar shi da kuma yin suka ga mai shari’an a fili.

“Sun ce kudin da aka dawo dasu daga gurin Abacha, na bayar da lissafi akai, wani irin wawanci ne! mutumin da yayi tambaya a kai, mutumin da ya yanke hukunci ko kuma wadda ya amsa dukkan su wawaye ne, babu tantama.

“Bana ajiye lissafi; dukkan kudin da aka dawo dasu daga gurin Abacha an tura su bankin duniya, kuma ko wani ragowa sai da aka sanar da ministan kudi…amma kuma, ya nuna jahilci, tsan-tsar jahilci, wandanda aka rasa kuma kuna mamaki, wadannan mutanan sunyi karatu kuwa?” tsohon Shugaban kasa yayi al’ajabi.

Lawyan yace masu shari’a basa yanke hukunci akan “son zuciyyoyisu” amma akan hujja da aka gabatar garesu da kuma bisa tsarin hukunci da shari’a ta tanadar.

“Da ace masu shari’a zasu dunga yanke hukunci akan ra’ayin yan siyasa ko wani, da za’a kaurace wa manufa na yan’cin kai da shari’a sosai.

Yace: “duk da yake yana daga cikin hakkin Obasanjoya saba wa shar’a ko kuma ya zarga da shi, ya kira Justice Idris “wawa da jahili” kawai domin yayi aikinsa, bai dace ba kamar yadda ya razana yancin da kuma mutuncin mai shari’ar ba.”

Wattani da suka wuce, Shugaba Muhammadu Buhari yace zai bayyana sunayen mutanan da suka yi sama da fadi akan ganiman da aka karbo na kudin jama’a. a halin da ake ciki, wasu nayin siyasa ya sa Obasanjo yayi gargadi ga Shugaban cewa kiran sunaye akan kudin da aka karbo zai iya sa kasar cikin rikici.

Asali: Legit.ng

Online view pixel