Tsohon shugaban kasa Jonathan ya dawo gida Najeriya

Tsohon shugaban kasa Jonathan ya dawo gida Najeriya

Tsohon shugaban kasa Dr Goodluck Ebele Jonathan ya dawo gida Najeriya bayan ya shafe kusan watan daya yana ziyaran Kasan Ingila da cote d'ivoire.

Tsohon shugaban kasa Jonathan ya dawo gida Najeriya
Former president Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban kasan ya sauka a babban filin saukan jirage dake portharcourt sannan ya zarce zuwa garinsa otueke a jihar Bayelsa.

KU KARANTA: Hotunan mataimakin shugaban kasa da Gwamna Rivers

A kwanakin bayannan jama'a ana ta radi radin cewa tsohon shugaban kasan yaje neman mafuka a kasar waje kasa hukumar EFCC ta kame shi a visa zargin almundahana da kudin kasa musamman kudaden sayo makaman hafsoshin sajojin Najeriya.

Tshohon shugaban kasan ya musanta wannan zargi kuma ya jaddada cewa yaje ziyara ne da kuma samun hutu a kasashen da ya ziyarta.

Hukumar EFCC tana binciken manyan jami'an gwamnatin data shude kuma da karban kudade daga gare su.

Tsohon shugaba Obasanjo ya shawarci shugaba Buhari akan kada ya bayyana sunayen wadanda aka samu kudaden a hannunsu gudun samun tsiko a yakin kawar da chin hanci,rashawa da almundahanar kudaden al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel