Yan Sanda sun kulle Ofishin jam'iyyar PDP na kasa

Yan Sanda sun kulle Ofishin jam'iyyar PDP na kasa

- Yan sanda sun kulle Ofishin jam'iyyar PDP na kasa akan rikicin shugaban ci

- An canza Yan sandan da suke gadin Ofishin jam'iyyar

- Sheriff ya hakikance kan cewa shine shugaban jam'iyyar

Yan Sanda sun kulle Ofishin jam'iyyar PDP na kasa
Mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP Ali Modu Sheriff

Rikicin shugabanci na jam'iyyar PDP ya sake shiga wani sabon mataki inda jami'an yan sandan Najeriya suka kulle Ofishin jam'iyyar dake a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, a ranar Lahadi 22 ga watan mayu na 2016, inda suka hana jami'an kwamitin gudanarwa na kasa.

Wannan yazo ne bayan da jam'iyyar ta gudanar da taron zabar sabon shugaban jam'iyyar na kasa guda 3 a lokaci daya inda aka gudanar da guda 2 a Abuja, da kuma daya a Fatakwal.

A cewar jaridar Premium Times, jami'an yan sandan sun kulle duka hanyar dake zuwa Ofishin na jam'iyyar PDP inda suka hana kowa shiga Ofishin sannan kuma aka canza yan sanda dake wurin.

Legit.ng ta ruwaitocewa an gudanar da taron guda 2 a Abuja inda anan aka zabi tsohon mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Ibrahim Mantu a matsayin sabon shugaban jam'iyyar, sannan kuma a fatakwal suka cire Ali Modu Sherif inda suka zabi Sanata Ahmed Makarfi, tsohon gwamnan jihar Kaduna a matsayin sabon shugaban jam'iyyar ta kasa.

Idan za'a iya tunawa, kimanin watanni 2 ke nan da jam'iyyar PDP ta nada Sanata Ali Modu Sheriff a matsayin mukaddashin jam'iyyar PDP. Wannan ya sanya wasu manyan jam'iyyar sukayi barazanar fita daga jam'iyyar domin su basu amince da shugabancin Ali Modu Sherif ba. Wasu sun zarge shi da shigowa jam'iyyar domin ya lalata ta don sun bayyana cewa jam'iyyar APC yake yi ma aiki.

A wani labarin kuma, kungiyar Bring Back Our Girls ta bayyana cewa Sarah Luka da sojojin Najeriya suka cet daga dajin Sambisa bata daga cikin yan matan Chibok 219 da kungiyar Boko haram ta sace. Wannan ya sanya aka nemi da hukumar soji ta kara bada bayanai domin tantance gaskiyar lamarin da kuma matsayin yarinyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel