Boko Haram: An gano daya daga cikin Yan matan Chibok

Boko Haram: An gano daya daga cikin Yan matan Chibok

- An gano daya daga cikin yan Matan Chibok da Boko haram ta sace

- Ta haihu kuma mijinta kwamandan Boko Haram ne

- An mika ta ga gwamnan Jihar Borno

Boko Haram: An gano daya daga cikin Yan matan Chibok
Amina Ali, wadda Boko Haram ta sace daga Chibok, rike da diyar ta tare da Gwamna Shattima

 

An gano daya daga cikin yan matan Chibok wadanda Boko haram suka sace. An same ta ta haihu kuma tane tare da wani mijin ta wanda Kwamanda ne a kungiyar Boko Haram. Sunan mijin nata Muhammad Hayatu.

KU KARANTA: Kungiyar Kungiyar Kwadago ta shirya cigaba da yajin aiki

Bayan da akla duba lafiyar ta data yaronnata, sai aka mika ta ga Hedikwatar lafiiya  dole duba cigaba da gudanar da bincike. Bayan da aka gama binciken, sai Kwamandan Birigade din Birigidya janar Victor Ezugwu, ya mika ta ga hannun gwamnan jihar Borno, Kashim Shattima.

Ana tsammanin Gwamnan zaya kawo ta Abuja da ita da iyayen ta domin ganawa da shugaban kasa Muhammadu buhari.

Shi kuma mijinta Muhammad hayatu ana cigaba da gudanar da bincike a kanshi. Amma rahotannin na nuna cewa sojojin sun karbe shi ba tare da buu ba kamar yadda suka shirya a tsarin lafiya dole akan baza su musguna ma yan ku giyar ba wadanda suka mika kansu ga hukuma.

Amina Ali Nkek dai yar asalin mbalala ce. Kuma Civilian JTF ne suka gano ta. Tana daga cikin Yan Mata 219 wadanda kungiyar Boko Haram ta sace tun 14 ga watan Afrilla na 2014. Daga lokacin izuwa yanzu, ita kadai ce wadda aka gano alhali sauran ba'a san inda suke ba.

A jiya laraba ne aka hada ta da iyayen ta inda BBc Afirika ta ruwaito cewa Maman ta ta rungume ta sosai. tayi godiya ga Allah daya hada su tare.

Mallam Garba Shehu, jami'i mai hudda da jama'a na shugaban kasa Buhari, ya bayyana cewa a yau shugaban kasa Muhammadu buhari zaya gana da yarinyar. Gwamna kashim Shattima ne zaya kawo ta fadar shugaban kasar.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa rashawa da satar cudin jama'a ne ya sanya gwamnatin Najeriya bata murkushe kungiyar Boko Haram tuni ba. ya bayyana wannan ne a jiya inda yake karbar bakuncin babban Malamin jami'ar AlAzhar dake Misira a jiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel