Darajar Naira ta daga akan Dala bayan da Nairar ta kare

Darajar Naira ta daga akan Dala bayan da Nairar ta kare

Darajar Naira ta karu bayan da Naira ta koma N360 akan Dala 1, inda a yanzu ta koma N343 akan Dala guda 1.

Darajar Naira ta daga akan Dala bayan da Nairar ta kare

A ranar Litinin data wuce, Naira ta kai har zuwa N367 akan Dala guda 1. Amma a yau an wayi gari Dala 1 tana a Naira 348.

Magiyar mu ta bayyana cewa "A garin Abuja, Dalar tana a N348 ne wanda hakan daya yake da Katsina sa wasu wurare. Amma duk da haka ba sauri muke mu saida ta ba domin har yanzu ana gudu neman a sayi dalar.

Nairar wadda ta kare a ranar Juma'a 13 ga watan Mayu inda ta kai har N367 ta dawo a jiya 16 ga watan mayu akan N348 a duk Dala 1.

Shugaban kungiyar masu canjin kudi na kasa, Alhaji Aminu Gwadabe, ya bayyana cewa har yanzu ana bukatar Dala sosai. Amma muna fatan cewa canjin kudin zaya daidaita cikin kwanakin nan.

Wanna na zuwa ne bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattabatawa kasafin kudin najeriya na 2016 hannu inda tuni gwamnatin najeriya ta bayyana cewa za'a saki makudan kudade domin a fara aiyuka wadanda zasu taimaka ma tallalinarzikin Najeriya kuma su rage ma talakawa radadin talauci da rashin da yake damun wasu yan Najeriya.

Shugaban kasa Buhari kuma ya sha alwashin ba yan najeriya Miliyan guda Daya Naira N5000 a duk wata. Amma mutanen da za'a bawa sai wadanda suka fi kowanne talauci da shiga halin kakanikayi a cikin al'ummar Najeriya.

A wani labarin kuma, karin farashin mai da gwamnatin Najeriya tayi ya sanya Dala ta tashi inda har ta kai N367 a shekaran jiya.Tuni yan kungiyar kwadago ta Najeriya ta bayyana cewa a yau talata 17 ga watan 2016, za'a shiga yakin aikin domin jan hankalin gwamnati data maido da tallafin mai kamar yadda yake.

Kungiyar ta bayyana cewa gwamnati bata kara ma ma'aikata kudade ba amma ta kara farashin Mai wanda hakan zaya jawo da hawan farashin kayan masarufi musamman a wannan lokaci da darajar Naira ke cigaba da karewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel