Manyan APC guda 5 da suka cancanci Buhari ya baiwa mukami

Manyan APC guda 5 da suka cancanci Buhari ya baiwa mukami

Kusan shekara guda kenan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau karagar mulki a karkashin tutar jam’iyyar APC da har wasu yan jam’iyyar sun fara kokawa a kan gazawar shugaban na janyo ‘yan jam’iyyar APC da shigo da su gwamnatin tasa a dama da su.

Manyan APC guda 5 da suka cancanci Buhari ya baiwa mukami

 

Sun nuna damuwar su ga yanda shugaban yafi bada mahimmaci a kan yaki da almundahana, gyara tattalin arzikn kasa da kuma cika alkawarurrukan da yayi wa mtanen Nijeriya fiya da gyara siyasar ta sa.

Wannan halin da shugaban yake ciki ta bar da yawa da ga cikin yan jam’iyyar da tamtamar ko shugaban zai juyo hankalin sa ga wandanda suka taka rawar gani a wajen tabbatar da takarar ta shi ta cimma nasara. Legit.ng ta kawo muku mutane guda 5 da suka cancanci a basu mukami saboda rawar da suka taka a wajaen takarar ta shugaba Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: Ajandar yaki da rashawa guda 7 na Buhari

1. Olurinimbe Mamora: Mamora dan shekara 63 shi ne ya rike mukamin mataimakin daraktan ayyuka na kampen din APC kafin zaben na 2015 kuma ya tsaya agefen shugaba Muhammadu Buhari da mataimakin sa Yemi Osinbajo zuwa kowani lungu da sako da sakon da suka shiga yayin da suke kampen.

Mamora dai gogaggen dan siyasa ne wanda Buhari zai mora sosai idan a ka bashi mukami. Ya rike mukamai da dama wadanda suka hada da chairman na kungiyar taro ta majalisar jiha

ta kasa daga shekara 2000 zuwa 2003, yayi senata sau biyu, yayi member na kwammitin man fetur, lafiya, da harkokin kasa da kasa na majalisar dattijai da sauransu.

2. Sam Nda-Isaiah: Shahararaen dan kasuwa ne. Mutane da dama sunyi mamaki lokacin da ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben fidda gwani na jamiyyar APC. Dalili kuwa shine, an san shi a matsayin dan gani kashe nin Buhari wanda harya kai ga Sam tare da wasu yan tsirarun mutane sun kafa kungiyar yan Buhari (The Buhari Organisation TBO). Yana daya daga cikin wadanda suka kafa CPC kafin a gamata a cikin APC. Sam dan shekara 54 ne a halin yanzu.

3. Osita Okechukwu: Shine bakin APC a yankin kudu maso gabashin kasar nan inda yake nuna matukar kwazo da hazaka a wajen aikin sa. Shima dan gani kashe nin Buharine kuma ya taka rawar gani wajen daga darajar APC a yankin. Bugu da kari, yayi sunane a matsayin sa na dan siyasa maikishin talakawa. Shine ya jagoranci CPC a commiting majar da ta haifar da kafa jam’iyyar APC

4. Umana Okon Umana: Yayi gagarumin yaki wajen tabbatar da cewa APC ta samu gurin zama a jahar Akwa Ibom a yankin kudu maso kudu nakasar nan. Umana dan shekara 56 ya rike mukamai a jahar daga matakin local gwamman har mataki na jaha.

Ya rike mukaman sakatare na social democratic party (SDP) a Ikono Local Gwamman a shekarar 1991, offisan zabe na Etinan Local government a shekarar 1996, kwamishinan kudi na Akwa Ibom a lokacin mulkin gwamna Victor Attah daga shekara 2003 zuwa 2007, dakuma sakataren gwamnatin Akwa Ibom a karkashin gwamnatin gwamna Godswill Akpabio

5. Ibrahim Dasuki jalo-Waziri: Shine shugaban matasan APC na kasa. Dan siyasa ne na gado wanda ya biyo sawun iyayen sa. Ya rike mukamin mai bada shawara na musamman a karkashin gwamnatin Danjuma Goje na jahar Gombe, a shekara 2004, yayi nasara zama charirman na gombe local government. A shekarar 2008 haka kuma an zabe shi a matsayin chairman na kungiyar local gwannoni nakasa wanda takunshi duka local gwannoni 774 na kasar nan.

Ya cimma nasara wajen gyara tsarin sadarwa tsakanin matasa da dattijun jam’iyyar APC da kuma hado kan matasan kasarnan a karkashi jamiyyar APC. Shima ya taka rawar gani a lokacin kamfen na zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel