Ni ba barawo bane, Femi Fani Kayode ya gaya ma EFCC

Ni ba barawo bane, Femi Fani Kayode ya gaya ma EFCC

-Femi Fani Kyode ya bayyana cewa ya gaya ma hukumar Efcc cewa shi ba barawo bane

- Hukumar ta aiak ma Femi Fani Kayode goron gayyata bayan da hukumar tayi ikirarin cewa ya gudu ya buya

Ni ba barawo bane, Femi Fani Kayode ya gaya ma EFCC
Femi Fani Kayode

Femi Fani Kayode, tsohon ministan jirgin sama , kuma Daraktan watsa labarai na kungiyar neman yakin zaben Jonathan a 2015, ya bayyana ma hukumar EFCC cewa shi ba Barawao bane. A yau ne ake tsammanin cewa tsohon Ministan zaya gurfana a hukumar domin ya amsa wasu tambayoyi.

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun kashe Yan Boko Haram, sun kwace makaman su

Femi Fani Kayode, wanda ake kira da FFK, an kira shi ne domin yayi bayani akan rawar daya taka wajen rarraba Dala Miliyan 115 wadda tsohuwar Ministar Mai, Diezani, ta bada a lokacin zaben 2015.

Hukumar EFCC ta bayyana cewa FFk yafi kowa morar kudaden inda ya samu Naira Miliyan 840 wadanda aka saka cikin Akwunt dinshi guda 3 dake a Bankin Zenith mai lamba 1004735721.

FFK ya samu gayyatar ta musamman bayan da hukumar tayi ikirarin cewa ya guda ya boye.

 

BAYANIN DA YAYI A BAYA

 

A bani dama in fara rubutun wannan makon da bayyana cewa a ranar 9 ga watan Mayu zani fita in bar gida na inda zani je hukumar EFCC domin inyi bayanin rawar dana taka a lokacin yakin neman zabe na shugaban kasa daya wuce.

Ni bani jin wani tsoro akan abunda hukumar zata ce ko kuma zata yi mani. Ina mai yin amfani da wannan domin inyi masu bayani akan abubuwan da zasu tambaye ni. Duk abunda suka ga dama sukayi mani, abun jin dadi ne a waje na.

Ko in kula shine keda sauki, amma aiki babban akwai kalubale. Ni ban damu akan abubuwan da suke faruwa kusa dani ba, da kuma zalunci da rashin adalci da akeyi.

Ni ba barawo bane. Nayi aiki a karkashin Jonathan domin inyi ma kasa hidima ba domin in amfana da ita ba.

Babu wani takaici da zanji domin mun fadi zabe ko kuma akn abubuwan da za'a yi mani. Iyaka dai kada a fita daga cikin tsari na mutuntaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel