Manyan labarai wadanda sukayi fice a ranar Litinin

Manyan labarai wadanda sukayi fice a ranar Litinin

Legit.ng ta tattara maku manyan labarai guda 10 wadanda sukayi fice a ranar Litinin 2 ga watan Mayu na 2016. Ku duba domin ku samu wadannan manyan labaran.

Manyan labarai wadanda sukayi fice a ranar Litinin
Buhari da Ministocin shi a wanin taro

1. Shugaba Buhari ya fusata, ya fita daga taron Ministoci

Rahotanni na nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fusata inda ya fita daga taron Ministoci bayan da suka bukaci ya kara masu kudaden gidajen haya.

KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya maganta akan hare-haren Fulani

2. Mutanenn Magboro sunyi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari

Al'ummar Najeriya na cigaba da korafi akan wahalhalu da suke fama da ita. Amma mutanen Magboro dakwe cikin Jihar Ogun abun nasu yayi tsanani.

3. 2Baba ya maganta akan zargin yin lalata da Tiwa Savage

Bayan zargin da mijin Tiwa Savage yayi ma 2 Baba akan lalata da matar shi, Mawakin ya maganta akan hakan.

4. Sarkin Musulmi ya maganta akan hare-haren da Fulani ke kaiwa

Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar na Ukku, ya maganta akan hare-haren da Fulani ke kaiwa a fadin Naeriya inda ya nemi a hukunta masu laifi kuma a zauna lafiya.

5. Sojojin Najeriya sun kama wadanda suka kashe Mamman Shuwa

Sojojin Najeriya sun kama wani wanda ake zargin cewa yana da hannu wajen kashe Janar Mamman Shuwa.

6. Hoton wani Mutum wanda Fulani suka raunata

Hoto ya fito na wani mutum wanda Fulani suka raunata bayan da suka kai hari a Ukpobi Nimbo dake a Uzo-Uwanni a Jihar Enugu.

7. An kashe Makiyaya 20, Shanu 83

A cikin manyan abubuwan dake cigaba da aikuwa, matasa Agatu sun kashe Makiyaya 20 inda suka halaka Shanun su 83. Wannan ya fito ne daga bakin shugaban garin Loko dake a Jihar Nasarawa.

8. Wani magidanci yayi ma wata ciki a Zimbabwe

Bayan yin lalata da wata karuwa, an kama wani magidanci da yi mata ciki

9. An kama wani mutum a Anambara da zargin kashe kanin shi

Rundunar yan sandan Jihar Anambara sun kama wani mutum mai suna Chukwudi Mmaduakor daga Ibughubu, akan zargin kashe kanin shi dan shekara 18, da kuma binne shi tare da taimakon abokan shi guda 2

Asali: Legit.ng

Online view pixel