IPOB: Kanu yayi hasashen Fulani zasu shiga kasar Igbo

IPOB: Kanu yayi hasashen Fulani zasu shiga kasar Igbo

- Kungiyar IPOB ta bayyana cewa Shugaban kungiyar Nnamdi Kanu yayi hasashen cewa Fulani zasu mamaye kasar Igbo idan Buhari yaci mulki

- Kungiyar ta bayyana cewa daman shugaban kungiyar ya bada gargadi akan Muhammadu Buhari amma aka ki ji

- Jami'in kuniyar Emma Powerful ya bayyana cewa Fulani naso su musluntar da kudancin Najeriya ne

IPOB: Kanu yayi hasashen Fulani zasu shiga kasar Igbo

Kungiyar IPOB tayi Allah wadai da hare-haren da Fulani suka kai a Uzo-Uwanni dake jihar Enugu inda suka kashe kimanin mutane 40.

Kungiyar IPOB ta bayyana cewa wannan yana daga cikin dalilan daya sanya suka kare dagewa akan dole a samar da kasar Biafra, Jarida Vanguard ta ruwaito.

KU KARANTA: Sojoji sun ga abun mamaki a sansanin yan Boko Haram

Kungiyar ta bayyana cewa daman tuni shugaban kungiyar IPOB, Nnnamdi Kanu, yayi hasashen aukuwar hakan. Ya kuma bayyana cewa daman sun bada gargadi akan shugabancin gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Emma Powerful ya bayyana haka a jiya Asabar 30 ga watan Afrillu.

yace " Zasu zo domin su tabbatar da shugabancin Hausa/Fulani akan mu. Zasu kori duka mutanen mu dake cikin Gwamnati. Za'a ba Fulani makamai su zo suna kashe mutane, manyan su zasu kare su.

" Fulani zasu shigo kudancin najeriya a cigaba da kokarin musuluntar da mutanen kudu maso Gabas. Za'a amshe kasar mu da sunan za'a bude hanyar makiyaya, daga mu kuma mun zama bayin su.

A gab da zabe kungiyar IPOB ta bayyana cewa duka da Jonathan da Buhari babu wanda zaya iya mulkin Najeriya a cikin su. Sun bayyana cewa Jonathan yana da rauni sosai, sh kuma Buhari mai tsanani ne. A cewar kungiyar, daman sun fadi cewa za'a saki wata kungiya wadda zata fi boko Haram kisa, zata yi kokarin lalata kudu maso gabas.

IPOB ta bayyana cewa baza ta canza matsayar ta ba akan cigaba da neman kasar Biafra ba tare da shubda jini ba. Wasu kungiyoyi da dama a kudu masi Gabas sun ba kabilar Hausa/Fulani wa'adin wani lokaci su bar yankin ko kuma su fuskanci ramuwa.

Tuni dai kungiyar Fulani ta bayyana cewa baza ta bar yawo da dabbobin ta ba a ko ina a Najeriya. Ta bayyana cewa wannan ya saba ma dokar kasa kuma babu wanda ya isa ya hana ta.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel