Abunda sojojin Najeriya ke shirin yima yan Bindiga dadi

Abunda sojojin Najeriya ke shirin yima yan Bindiga dadi

- Hukumar soji ta bayyana cewa ta ware runduna ta musamman domin maganin makiyaya masu kashe mutane

- Sun bayyana cewa duk wanda aka kama da laifi za'a hukunta shi kamar dan Boko Haram ko kuma tsageran Nija Delta

- Wasu wadanda ake zargin cewa Fulani ne suna yawo suna karkashe mutane a wurare daban daban

Abunda sojojin Najeriya ke shirin yima yan Bindiga dadi
Wani makiyayi da Bindiga kirar AK-47

Birigidiya janar Rabe Abubakar, Mukaddashin Daratan Labarai na hukumar sojin Najeriya, ya bada gargadi akan a unda wasu mutane wadanda ake zargin Fulani ne da kashe mutane a Ukpabi-Nimbo dake a karamar hukumar Uzo-Uwani.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sunyi artabu da yan Boko Haram a Wumbi

Daraktan ya bayyana cewa hukumar soji a shirye take da ta dauki mataki akan masu aikata hakan.

Daraktan ya bayyana cewa sojoji zasu hada kai da Yan sanda don da sauran jami'an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a fadinn Najeriya, wanda shine babban kalubale ga Gwamnatin  Tarayya a karkashin shugaban kasa Muhammadu buhari.

yace " Idan zaku iya tunawa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bamu umurni wanda kuma dole mu bi kamar sauran, inda yace a kawo karshen kashe-kashen. mun kai mutanen mu wurare inda muka yima aikin suna da "Sharan daji" domin tabbatar da cewa makiyaya basu shiga cikin aikata laifuka ba.

" Muna ta kokari kuma muna samun nasarori. Jami'an tsaro ba zasu iya kulle idanun su ba daga abubuwan da suke faruwa.

Ya bayyana cewa sha'anin tsar ba abu bane wanda za'a bari lamarin siyasa ya shigo ciki ba. Ya kuma shawarci mutane dasu hada kai da jami'an da aka kai wuraren su domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.

" Na san cewa an sanar da shugaban hafsin sojin najeriya, nayi imani cewa nan bada jimawa ba zamu fiddo da wani shiri domin hanu su aikata barna a wuraren a fadin Najeriya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel