Ku yi magudi a zaben Anambra, ku mutu a hatsarin jirgin sama – Fasto ta gargadi ‘yan siyasa

Ku yi magudi a zaben Anambra, ku mutu a hatsarin jirgin sama – Fasto ta gargadi ‘yan siyasa

  • ‘Yan makonni kadan suka rage kafin zaben gwamnan Anambra, amma tuni wasu ‘yan siyasa suka fara yunkuri don cimma manufarsu na gashin kansu
  • Tseren na kara karfi amma Fasto Dr Misis Flora Ilonzo ta yi kira ga ‘yan siyasa, ta nemi da su guji yin magudi a zaben da za a yi a ranar Asabar, 6 ga watan Oktoba
  • Malamar ta shawarci ‘yan siyasa da su ci gaba da kasancewa a jam’iyyarsu, inda tace idan suka ki jin gargadin, annoba na jiran su

Awka, Anambra - Shugabar cibiyar kula da lafiyar kwakwalwa ta CPHA, Flora Ilonzo ta shawarci 'yan siyasa da ke shirin yin magudi a zaben ranar 6 ga watan Nuwamba, a jihar Anambra da su manta da irin wannan tunani.

A cewarta, duk wanda ya yi magudi a zaben zai iya mutuwa mai radadi a hadarin jirgin sama. Ta ce gargadin ya zama dole saboda kowa na bukatar sanin sakamakon irin wannan matakin, jaridar The Sun News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben APC: Ministoci, Hadimai da manyan ‘Yan Majalisa suna cikin matsala a wasu Jihohi

Ku yi magudi a zaben Anambra, ku mutu a hatsarin jirgin sama – Fasto ta gargadi ‘yan siyasa
Ku yi magudi a zaben Anambra, ku mutu a hatsarin jirgin sama – Fasto ta gargadi ‘yan siyasa Hoto: Flora Nkemakonam Ilonzo
Asali: Facebook

Ta gargadi ‘yan siyasa da ke sauya sheka daga wannan jam’iyya zuwa waccan da su gaggauta komawa tsoffin jam’iyyunsu kafin zaben ranar 6 ga watan Nuwamba ko kuma su shirya ganin duhu harma a cikin ahlinsu.

Ta ce:

“Ina so in yi kira ga iyalan ‘yan siyasa da su gargade su da su daina tsalle daga wannan jam’iyya zuwa waccan. Idan ba haka ba, fushin mutane da na Allah zai kasance a kansu nan ba da jimawa ba.
“Kuma abun zai fi shafar iyalan saboda wadannan ‘yan siyasan ba lallai ne su kasance a kasa ba lokacin da za a kai hari gidajen nasu. Don haka, ya ragema ‘yan siyasa da suka kagu su yi taka-tsan-tsan. Iyalan ‘yan siyasa da suka kagu su yi hankali sosai sannan su shawarci masoyansu.”

Kara karanta wannan

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

Ilonzo, wacce ta kuma gargadi 'yan siyasa kan yin amfani da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ko 'yan daba don sauya sakamakon zaben, ta ce fatalwar mutanen da aka kashe da jefar da su a Kogin Ezu da wadanda rikicin rusasshiyar rundunar SARS ta cika da su suna kukan adalci.

Ta ce:

“Ina hango Karin kashe-kashe da ke zuwa a jihar Anambra da sauran jihohin kudu maso gabas. ‘Yan siyasa su yi hankali kan yadda suke tsalle daga wannan jam’iyyar zuwa wata. Fushin Allah da na mutanen da aka kashe ba bisa adalci ba suna yawo a unguwa don daukar fansar mutuwarsu.
“Abun da ke faruwa a jihar Anambra da sauran jihohin kudu maso gabas ba haka kawai bane. Na yi hasashe a baya game da lamarin ‘yan bindigar da ba a san ko su wanene ba amma babu wanda ya saurare ni.”

APGA ta yi martani, ta bayyana dalilin da yasa mataimakin gwamnan Anambra ya sauya sheka zuwa APC

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Shekarau ya bayyana makasudin kai korafin Ganduje gaban Shugabannin APC na kasa

A wani labarin, mun kawo a baya cewa Jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) ta yi martani a kan sauya shekar mataimakin Gwamnan jihar Anambra, Dr Nkem Okeke, zuma jam’iyyar All Progressives Congress.

A wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba, sakataren jam’iyyar APGA na kasa, Tex Okechukwu, ya ce matakin mataimakin gwamnan ba zai girgiza jam’iyyar ba gabannin zaben gwamna na ranar 6 ga watan Nuwamba.

Ya kara da cewa sauya shekar abu ne da aka dade ana tsammani tun da Okeke na ta gaba da kowa kan rashin samun tikitin takarar gwamana na jam’iyyar, Channels TV ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel