Hadimin da Ganduje ya sallama daga aiki yace burki ya tsinkewa Gwamnan jihar Kano

Hadimin da Ganduje ya sallama daga aiki yace burki ya tsinkewa Gwamnan jihar Kano

  • Mu’azu Magaji yace ya ji dadin tsige shi daga shugaban aikin AKK da aka yi
  • Dansarauniya ya bayyana cewa ya dade yana tunanin yadda zai yi murabus
  • Shugaban tafiyar Win-Win yace burki ya tsinkewa Gwamnan Kano Ganduje

Kano - Muazu Magaji ya yi maganganu da samun labarin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tsige shi daga shugaban kwamitin aikin birne gas na AKK.

Da yake maida martani a shafinsa na Facebook, Injiniya Muazu Magaji yace ya ji dadi da aka raba shi da wannan nauyi da ya yi ta tunanin ajiye wa da kansa.

Injiniya Magaji yake cewa saboda gudun a ce ya yi watsi da dawainiyar al’umma da kuma ganin girman Gwamnan Kano ya cigaba da rike wannan kujerar.

Kara karanta wannan

Tunde Bakare ya yi magana game da shirin takarar 2023 bayan ya sa labule da Buhari

“Na rantse da Allah da ya halicce ni, na yi tunanin barin aikin nan yafi a kirga, saboda dalilai da dama...Tunda ai dama cikin sirri na bar aikin Executive Director project...
Shima saboda dalilai masu nauyi...amma kan AKK saboda kada ya zamana mun juyawa Kanawa baya akan abinda zamu iya na taimaka musu...ko ace munyi butulci ga HE AU Ganduje yasa muka daure...muna adduar Allah dai ya fitar damu lafiya.” - Muazu Magaji

Hadimin Ganduje
Muazu Magaji da Gwamna Ganduje Hoto: @Muaz Magaji
Asali: Facebook

Uban kuturu ya yi kadan

Magaji yace ba yau ya saba jin kalmar ‘tsigewa’ ba, a cewarsa, babu wanda ya isa ya tuhume shi da rashin kokari, kamar yadda aka zarge shi da aka sallame shi.

Daga baya kuma an ji Dansarauniya yana godiya ga Allah, yana cewa gobe zai tashi babu nauyi a kansa.

Kara karanta wannan

Zargin batanci: Rikici ya barke tsakanin Sheikh AbdulJabbar Kabara da Lauyoyinsa a Zaman Kotu

“Masha Allah! Alhamdulillah Wallahi I am relieved! Gobe in Allah ya kaimu zantashi a free man!” - Muazu Magaji

Tsohon kwamishinan yace sallamarsa da gwamna Ganduje ya yi, zai ba shi damar cigaba da siyasar gwagwarmaya domin karbo wa mutanen jihar Kano ‘yanci.

Burki ya tsinkewa Ganduje, ya zama abin tausayi

Har ila yau, Dansarauniya ya yi amfani da shafin na sa yana cewa tun da burki ya tsinke wa Baba (Ganduje), yanzu za su dage wajen karbe ikon jam’iyyar APC a Kano.

"Dama zaman tare ne da HE AU muke kokarin ceto Jamiyyarmu ta APC...Tunda Birki ya tsinkewa Baba, yanzu sai mu kauce kada jini ya bata mana fararen kayan mu!" - Win-Win

Injiniya Magaji yace a jira sanarwa a kan matakin da zai dauka a siyasance, ba tare da tada rikici ba.

"Alhamdulillah! A jira sanarwa Kan matsayin mu a siyasa...Amma dai bata tsiya tsiya ba!" - Magaji

Kara karanta wannan

Sojoin Najeriya sun hallaka kasurgumin dan bindiga da yayi tuban muzuru, Alhaji Karki

A ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba, 2021, sai aka ga Magaji ya rubuta cewa gwamna Abdullahi Ganduje yana ba shi tausayi, ganin yadda siyasar Kano ta ke sake salo.

APC ta bangare a Kano

Idan ba a manta ba, ‘yan taware a Kano sun gabatar da koke-koke da korafai wajen uwar Jam’iyyar APC. Injiniya Muaz Magaji yana cikin 'yan wannan tafiyar.

Da suke jawabi ta bakin Ibrahim Shekarau, fusatattun 'ya 'yan na APC sun ce Gwamnatin Kano ba ta tafiya da Sanatocin da duk masu rike da mukamai a APC a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel