Babbar magana: Majalisar dokokin wannan jihar ta dakatar da yan majalisu biyu kan zargin alaka da yan bindiga

Babbar magana: Majalisar dokokin wannan jihar ta dakatar da yan majalisu biyu kan zargin alaka da yan bindiga

  • Majalisar dokokin Zamfara ta dakatad da mambobinta biyu kan zargin suna da alaƙa da yan bindiga
  • Sai dai dakatarwan ta tsawon watanni uku ne, lokacin da ake tsammanin kwamitin tsaro ya kammala bincike a kansu
  • Amma rahoto ya nuna cewa bita da kulle ake wa yan majalisun domin ɗaya na kokarin ficewa daga APC zuwa PDP

Zamfara - Majalisar dokokin jihar Zamfara ta bayyana dakatar da mambobin majalisar biyu bisa zarginsu da hannu a taimakawa yan bindiga.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jami'in dake hulɗa da jama'a na majalisar, Mustapha Jafaru Kaura, ya fitar ranar Talata.

BBC Hausa ta rahoto cewa majalisar ta dakatar da mambobin biyu ne na tsawon watanni uku zuwa lokacin da za'a gama bincike kan lamarin.

Kakakin majalisar Zamfara
Babbar magana: Majalisar dokokin wannan jihar ta dakatar da yan majalisu biyu kan zargin alaka da yan bindiga Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Majalisar ta umarci kwamitin ɗa'a da kuma na tsaro su gudanar da bincike kan wannan zargin da akewa mutanen biyu.

Kara karanta wannan

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane yan majalisa ne abun ya shafa?

Yan majalisun dokoki da lamarin ya shafa sune, Yusuf Muhammad Anka, mai wakilatar ƙaramar hukumar Anka da kuma Tukur Bakura, mai wakiltar Bakura.

Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa yan majalisun da ake zargin basa cikin zauren majalisar bare su maida martani kan lamarin.

Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Maru, Yusuf Alhassan Kanoma, shine ya gabatar da kudirin a gaban majalisar.

Wasu rahotanni daga majalisar sun nuna cewa ana yiwa yan majlisun biyu wannan zargin ne domin kokarin da ɗayansu yake na ficewa daga APC.

Meyasa majalisa ta ɗauki wannan matakin?

Wani sashin sanarwar da majalisar ta fitar yace:

"Majalisa ta samu labarin cewa Yusuf Muhammad Anka da Ibrahim T Tukur Bakura, suna farin ciki da sace mahaifin kakakin majalisa."

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya ware Naira miliyan miliyoyi, zai biya kudin karatun yara 600 a garuruwan Legas

"Kuma mun samu bayanan sirri kan cewa suna da hannu a kisan ɗaya daga cikkn mambobin mu mai wakiltar Shinkafi, bayan waya da maharan."

Daga ƙarshe majalisar ta umarci jami'an tsaro su bincike wayoyin yan majalisun na salula yayin gudanar da bincike kan zargin, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

A wani labarin kuma Kwastam ta kwace jarkoki 1,000 makare da man fetur za'a kaiwa yan bindiga a Katsina

Mukaddashin shugaban NCS reshen jihar, Wada Chide, shine ya bayyana haka a wurin taron al'umma da hukumar ta saba shiryawa don bayyana wa mutane halin da ake ciki.

Chide ya ƙara da cewar hukumar NCS tana haɗa kai da sauran hukumomin tsaro wajen tabbatar da doka da oda a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel