Manyan ƴan siyasan arewa 5 da suka yi rantsuwar ba za su sauye sheƙa ba amma suka saɓa

Manyan ƴan siyasan arewa 5 da suka yi rantsuwar ba za su sauye sheƙa ba amma suka saɓa

Akwai 'yan siyasa da dama da suka taba yin rantsuwar ko alkawarin ba za su canja jam'iyya ba amma daga bisani suka saba wannan alkawarin domin cimma wata manufa ta siyasa.

Daga cikinsu, akwai mataimakin shugaban kasa, gwamnoni, yan majalisa da sauransu kamar yadda ruwaiyar Daily Trust ta lissafo.

Wadannan 'yan siyasan ba sune kadai suka sauya jam'iyya ba amma abin da ya banbanta su da sauran shine sun dau alkawari a bainar jama'a cewa ba za su canja jam'iyya ba.

Manyan ƴan siyasan arewa 5 da suka yi rantsuwar ba za su sauye sheƙa ba amma suka saɓa
Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso da Aminu Waziri Tambuwal. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk da cewa doka bata hana canja jam'iyya ba, amma wasu masu nazarin harkokin siyasa na alakanta hakan da rashin alkibla ta siyasa da manufa a bangaren 'yan siyasan.

Kara karanta wannan

Atiku da Saraki na kitsa kwace PDP daga gwamnoninta, su sake dawo da Secondus

1. Atiku Abubakar

Na farko cikin wadanda suka karya alkawarinsu shine tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

Dan takarar shugaban kasa a 2015, Atiku, wanda ya taka muhimmiyar rawa wurin kafa jam'iyyar APC, ya ce, "

A lokacin da na zaga kasarmu na ji abubuwan da mutanen mu daga bangarori daban-daban ke bukata, na ce APC ne madakata, kuma shine karshen layin."

Amma yayin da ya ke komawa PDP a 2019, Atiku ya rera wata wakar yana cewa,

"Jam'iyyar da muka kafa ta gaza kuma tana cigaba da gazawa a idon mutanen mu, musamman matasa. Ta yaya shugaban kasa zai zabi 'yan fadarsa banda matasa? Jam'iyyar da bata yi da matasa za ta mutu. Matasa sune manyan gobe."

2. Aminu Waziri Tambuwal

Kamar Atiku, Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, a 2014, yayin da zai fice daga PDP ya koma APC, ya ce,

"Bisa damar da kundin tsarin mulkin 1999 ta bani da kuma duba da yadda PDP ta zama a jiha ta ta Sokoto, ina sanar da komawa na jam'iyyar APC."

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan daba sun yi wa babban jami'in APC duka har ya gigice, sun kona gidansa a jihar Nasarawa

Tambuwal, gabanin babban zaben 2019, bayan rikicinsa da mai gidansa, Aliyu Wamakko, ya ce,

"Saboda na gamsu cewa babu kasa da za ta iya cigaba a yayin da akwai rashin dai-daito da rashin mulki na gari; saboda rashin cancanta, lalaci da rashin yarda cewa rashin shugabanni na gari ya zama babban makamashin da ake tafiyar da Nigeria a yau."

3. Rabiu Musa Kwankwaso

Kwankwaso ya shafe shekaru da dama yana matsayin jigo a jam'iyyar PDP. An zabe shi gwamnan jihar Kano a karkashin PDP sau biyu a 1999 da 2011. A 2014, ya fice daga jam'iyyar ya koma APC.

A lokacin da ake jita-jitarcewa yana shirin komawa APC a 2017, Kwankwaso ya bayyana jita-jitar a matsayin 'labarin kanzon kurege'.

Shugaban ma'aikatan fadarsa, Aminu Abdussalam a lokacin ya ce: "Ba mu taba tunanin barin APC ba. Mun mi mamaki tare da bakin ciki a lokacin da muka karanta labarin."

Kara karanta wannan

Zamfara na fama da 'yan gudun hijira 700,000, gidaje 3,000 sun halaka, Matawalle

Amma daga baya ya sake komawa PDP. Yayin da yake komawa PDP ya kuma ce,

"Yanzu na samu 'yanci kuma ina da damar gwada sa'a na a ko ina.
Na san cewa PDP ce jam'iyya mafi girma, kuma idan sun bi tsarin demokradiyya, za a kayar da Buhari cikin sauki, amma idan suka tilastawa jam'iyyar dan takara, za su sha kaye.

4. Samuel Ortom

Manyan ƴan siyasan arewa 5 da suka yi rantsuwar ba za su sauye sheƙa ba amma suka saɓa
Gwamnan Benue Samuel Ortom. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Ortom, gwamnan jihar Benue mai ci a yanzu, ya shiga APC ne daf da babban zaben 2015 kuma ya ci zaben a karkashin inuwar jam'iyyar.

A lokacin, ya ce,

"Kowa ya sani cewa an tafka rashin adalci tunda farko kuma an shirya cutar mambobin jam'iyyar da dama da kuma a matakin mazabu, bayan kammala amfani da dukkan daman da ya rage a PDP, ya zama dole in gwada wata jam'iyyar."

Amma da abubuwa suka rikice masa, Ortom ya lashe amansa, yana cewa,

Kara karanta wannan

Gbajabiamila, gwamnoni da sauransu sun makure miliyoyin wurin ziyartar Tinubu

"Ina fuskantar matsaloli, kuma shugabannin jam'iyyar APC na kasa sun sani. Na tuntubi mazaba ta, ciki har da kansiloli 276 da suke nan. Baya ga shugaban karamar hukumar Tarka da ta ce za ta tuntubi wasu, dukkan sauran sun ce ba a maraba da ni a APC a yanzu."

5. Bello Matawalle

Manyan ƴan siyasan arewa 5 da suka yi rantsuwar ba za su sauye sheƙa ba amma suka saɓa
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Matawalle ya zama gwamnan Zamfara a 2019 bayan ya fadi zabe, sai dai ya taki sa'a saboda rikicin cikin gida na jam'iyyar APC da yasa kotun koli ta soke zaben APC.

A shekarar 2019, ya yi rantsuwar ba zai fice daga PDP ba, yana mai cewa,

"Idan har na ci amanan PDP, kada in zauna lafiya a sauran rayuwa ta, na rantse da Allah. Idan zan iya barin PDP ko in yaudari sauran mambobinmu, Allah ya hukunta ni."

Amma tuni ya koma APC. Matawalle, yayin da zai koma jam'iyyar mai mulki a Yunin wannan shekarar yace,

"Siyasa batu ne na jarumta da biyan bukata. 'Yan siyasa da dama sun sauya jam'iyya, saboda haka ba sabon abu bane. Na sauya jam'iyya don in kawo zaman lafiya a jiha ta."

Asali: Legit.ng

Online view pixel